Dalilin da Ya Sa Gwamna Abba Ya Mayar da Sanusi II Kan Kujerar Sarkin Kano

Dalilin da Ya Sa Gwamna Abba Ya Mayar da Sanusi II Kan Kujerar Sarkin Kano

  • A jiya Alhamis Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tsige Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano tare da maye gurbinsa da Muhammadu Sanusi II
  • Hakan ya faru ne bayan da majalisar dokokin jihar Kano a ranar Alhamis din ta tsige duka sarakuna biyar tare da soke masarautun jihar
  • A yayin da Gwamna Yusuf ya bayyana dalilin dawo da Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano, ya kuma ba korarrun sarakunan wa’adin sa’o’i 48

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya bayyana cewa mayar da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarki, cika alkawari ne na yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Duk da umarnin kotu, Gwamna Abba zai mika takardar nadi ga Sanusi II

Abba Yusuf ya yi magana kan mayar da Sanusi II gidan sarautar Kano
Gwamnan jihar Kano ya fadi dalilin sake mayar da Sanusi kan kujerar Sarki. Hoto: @Kyusufabba, @masarautarkano
Asali: Facebook

A jiya Alhamis muka ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar doka da ta rusa dokar majalisar masarautun jihar ta 2019.

"Dalilin sake nada Sanusi II" - Abba

Bayan kammala taron, gwamnan ya ce sabuwar dokar ta tanadi mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Yusuf ya ce:

"Bayan rattaba hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano a gidan gwamnati dake Kano, yau. Na ayyana Mai Martaba Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano."

Jim kadan kuma bayan kammala taron, jaridar PremiumTimes ta ruwaito mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar da sanarwa.

A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya ce mayar da Muhammadu Sanusi II gidan sarautar Kano na daga cikin alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da Sanusi II bayan Abba ya mayar da shi Sarkin Kano

"Kano ta koma masarauta 1" - Abba

Sanarwar ta ce:

“Ina so in sanar da mutanen Kano cewa a yau mun sake nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 yayin da tsofaffin sarakuna biyar za su bar fada cikin sa’o’i 48.
“Tsofaffin sarakunan za su mika duk kadarorin da ke hannunsu ga kwamishinan kananan hukumomi wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar.
"A karkashin sabuwar dokar da ta kafa masarautar Kano ta 2024, jihar Kano ta koma karkashin masarauta daya ne yanzu."

Sanusi II fice daga dakin taro cikin gaggawa

Tun da fari, mun rahoto cewa Sanusi II ya halarci taron tattalin arziki da zuba jari na jihar Rivers lokacin da aka samu labarin mayar da shi kan karagar mulki a matsayin Sarkin Kano.

An ce Sarki Sanusi II ya yi gaggawar ficewa daga dakin taron bayan jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel