Gwamna Abba Ya Sa Labule da 'Yan Majalisa, Masu Nada Sarki a Kano, Bayanai Sun Fito

Gwamna Abba Ya Sa Labule da 'Yan Majalisa, Masu Nada Sarki a Kano, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya labule da ƴan majalisar dokokin jihar da masu naɗa sabon Sarki
  • Ganawar gwamnan da mutanen na zuwa ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da sabon ƙudirin dokar da ya yi wa dokar kafa masarautun jihar garambawul
  • Ana sa ran Gwamna Abba zai rattaɓa hannu a dokar wacce ta rushe sababbin masarautun da aka ƙirƙiro a lokacin mulkin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shiga ganawar sirri da ƴan majalisar dokokin jihar a gidan gwamnatin jihar.

A ganawar da gwamnan ya shiga har da wasu masu riƙe da sarautun gargajiya da ake kyautata zaton masu naɗa Sarki ne.

Kara karanta wannan

Nadin Sanusi II: Abba ya ba korarrun sarakuna umarni a wa'adin awa 48

Gwamna Abba ya gana da 'yan majalisa a Kano
Gwamna Abba ya gana da 'yan majalisa a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ana sa ran gwamnan zai sanya hannu kan ƙudirin dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da shi tun farko a ranar Alhamis wanda ya rushe sababbin masarautu da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammad Sanusi II zai zama sabon Sarki

Idan Gwamna Abba ya sanya hannu kan wannan ƙudirin dokar, ana sa ran za a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, wanda aka tsige a watan Maris ɗin 2020, cewar rahoton tashar Channels tv.

Sai dai har yanzu ba a san makomar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ba.

Rahotanni sun ce Sarki Aminu Ado Bayero ba ya Kano a halin yanzu bayan da ya ziyarci Oba Sikiru Adetona, Awujale na Ijebuland, a ranar Laraba.

Gwamnatin Rabiu Kwankwaso ta nada Muhammad Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), a matsayin Sarkin Kano na 14 a watan Yunin 2014.

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

Gwamna Abba ya rushe masarautun Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sanya hannu kan dokar da ta rusa masarautun jihar.

Gwamnan ya sanya hannun ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu bayan mika masa takarda mai ɗauke da dokar a gidan gwamnatin jihar.

Rattaba hannu kan dokar ya sake tabbatar da rushe masarautun guda biyar da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel