Nadin Sanusi II: Abba Ya Ba Korarrun Sarakuna Umarni a Wa'adin Awa 48

Nadin Sanusi II: Abba Ya Ba Korarrun Sarakuna Umarni a Wa'adin Awa 48

  • Gwamnan jihar Kano ya umarci korarrun sarakunan Kano da su tattara ƴan komatsansu su fice daga fada
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin bayan ya rattaɓa hannu kan dikar da yi wa masarautun jihar Kano garambawul
  • Umarnin da gwamnan ya bayar dai ya shafi sarakunana biyar da aka naɗa a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya buƙaci sarakunan da aka tsige da su fice daga fada cikin sa'o'i 48.

Sarakunan guda biyar na jihar Kano sun rasa sarautunsu ne bayan garambawul ɗin da majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar kafa masarautun jihar.

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

Gwamna Abba ya ba korarrun sarakuna sabon umarni
Gwamna Abba ya umarci korarrun sarakuna su fice daga fada Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamna Abba ya tuɓe sarakuna a Kano

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Gwamna Abba ya ba tuɓaɓɓun sarakunan wannan umarnin ne bayan ya sanar da naɗin Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umarnin gwamnan dai ya shafi sarakuna biyar da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa.

Abba ya rusa nadin sarakunan Ganduje

Ganduje ya raba Masarautar Kano gida biyar sannan ya naɗa Sarki a kowace daga cikinsu.

Daga cikin sababbin masarautun da aka ƙirƙiro akwai Karaye, Gaya, Bichi sai kuma Rano.

Sai dai, majalisar dokokin jihar Kano da ke ƙarƙashin jam’iyyar NNPP ta soke dokar da Ganduje ya yi amfani da ita wajen yin waɗannan sauye-sauye.

Wane umarni Gwamna Abba ya ba da?

Da yake jawabi ga manema labarai bayan sanya hannu kan dokar, Gwamna Abba Yusuf ya umurci korarrun sarakunan da su tattara komatsansu.

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

Gwamnan ya kuma umarcesu da su miƙa komai da komai a hannun kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar cikin kwanaki biyu.

Sanusi II ya zama sabon Sarkin Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Muhammad Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano shekara hudu bayan an tsige shi.

Naɗin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar ta tabbatar haɗe masarautun jihar guda biyar da tsige dukkanin masu riƙe da muƙaman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel