Mafi Karancin Albashi: NLC ta Sauko Daga Bukatar N615,000, ta Fadi Sabon Tayi

Mafi Karancin Albashi: NLC ta Sauko Daga Bukatar N615,000, ta Fadi Sabon Tayi

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta yi fatali da tayin da gwamnatin tarayya ta yi na biyan ma'aikata N57,000 a matsayin mafi karancin albashi yayin da har yanzu aka gaza fahimtar juna
  • Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin kwadago sun yi ragi daga abin da suka nema tun da fari na N615,000 zuwa N497,000 domin bawa gwamnati damar biyan kudi
  • Rahotanni na bayyana cewa kwamitin gwamnatin tarayya kan duba albashin karkashin jagorancin Bukar Goni ya ce ba za su iya biyan kudin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- A fafutukar da Kungiyar kwadago ke yi na tilasta gwamnati biyan mafi karancin albashin da zai tabuka wani abu a rayuwar ma’aikata, yanzu haka ta sauko daga neman a biya N615,000.

Kara karanta wannan

Gwamna Lawal ya kafa tarihi, ma'aikata za su sha romon mafi ƙarancin albashi bayan shekaru

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta hada baki da bangaren masu zaman kansu wajen bayyana cewa za su biya N57,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Kungiyar NLC
Mafi karancin albashi: NLC ta rage buri zuwa 497,000 Hoto: Kola Sulaiman
Asali: Getty Images

Punch News ta wallafa cewa yanzu haka kungiya ta yi ragi daga N615,000 zuwa N497,000, inda suka yi fatali da tayin N57,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin gwamnati kan mafi karancin albashi?

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin da zai yi duba kan batun mafi karancin albashi da kungiyar NLC ke cewa ya yi kadan.

A zaman da ya gudana kan batun, kwamitin gwamnati karkashin Bukar Goni ya ce babu isassun kudin biyan kudin da NLC ta nema.

A bangare guda kuma kamfanoni masu zaman kansu ba su da kudin da za su iya biyan kudin, kamar yadda Vanguard News ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Mun ba ku mako 2," NLC ta ja kunnen jihohi kan biyan N30,000 a mafi karancin albashi

NLC ta sake watsi da tayin gwamnati

A wani rahoton mun kawo muku cewa kungiyar kwadago ta kasa NLC ta sake fatali da tayin mafi karancin albashi da gwamnati ta yi mata, inda ta ce ba za ta amince da kasa da abin da ta nema ba.

Gwamnatin tarayya ta ki amincewa da biyan N615,000 da hadakar kungiyoyin kwadago na NLC da na 'yan kasuwa TUC suka nema domin cicciba rayuwar ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel