29 Ga Mayu: Ministoci Na Cikin Matsala, Tinubu Ya Basu Umarni Kan Ayyukansu

29 Ga Mayu: Ministoci Na Cikin Matsala, Tinubu Ya Basu Umarni Kan Ayyukansu

  • Yayin da Bola Tinubu ke cika shekara daya a kan mulki, kowane minista zai gabatar da abin da ya tsinana ga ƴan kasa
  • Ministan yada labarai a Najeriya, Mohammed Idris ya bayyana haka a jiya Laraba 22 ga watan Mayu a birnin Tarayya Abuja
  • Idris ya ce babu wani gagarumin bikin da za a gudanar yayin cika shekara daya a kan mulki na Tinubu sai dai gabatar da nasarori da aka samu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo sabon tsari ga Ministocinsa yayin da yake cika shekara daya a karagar mulki.

Bola Tinubu ya umarci dukkan Ministoci 47 da su gabatar da abubuwan da suka cimma tsawon lokacin da suka rike mukamin ga ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan daka ya yi daka, Ministan Tinubu ya ba ƴan Najeriya hakuri, ya fadi shirinsu

Tinubu ya ba ministocinsa sabon umarni kan abin da suka tsinana
Bola Tinubu ya umarci ministocinsa su gabatar da abin da suka tsinana cikin shekara daya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Ministocin Tinubu za su fara nuna ayyukansu

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya tabbatar da haka a jiya Laraba 22 ga watan Mayu yayin wani taro a Abuja a cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce daga yau Alhamis 23 ga watan Mayu, Ministoci za su zo su bayyana abin da suka tsinana ga ƴan kasar a bayyane, cewar BusinessDay.

Gwamnatin Tinubu ta kashe biki

"Daga gobe (Alhamis) 23 ga watan Mayu, ministoci za su rika gabatar da abin da suka aikata na alheri a ma'aikatunsu ga ƴan Najeriya."
"Ba za muyi wani biki kan cika shekara daya na mulki ba sai dai gabatar da ayyuka da Ministoci suka yi."

- Mohammed Idris

Akume ya yi magana kan matakan Tinubu

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu sun samu halartar taron.

Kara karanta wannan

"Da wahala", Jigon APC ya gaji da kame kamen Tinubu wajen gyara Najeriya kamar Lagos

Sanata Akume ya bayyana irin tsare-tsaren Shugaba Tinubu inda ya ce za su inganta tattalin arzikin kasar.

Ya ce matakan da Tinubu ke dauka sun kara jawo hankulan masu zuba hannun jari daga ketare da rage tashin farashin kaya a Najeriya.

Tinubu: Minista ya ba ƴan Najeriya hakuri

Kun ji cewa ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya fito fili ya ba ƴan Najeriya hakuri kan halin da ake ciki a kasar a yau.

Bagudu ya ce sun san halin da ake ciki amma matakan da Shugaba Bola Tinubu ke ɗauka sun zama dole domin inganta tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel