Filato: Adadin Mutanen Zurak da Suka Mutu a Harin 'Yan Bindiga Ya Karu
- An kara samun mutane da suka mutu biyo bayan harin da yan bindiga suka kai kauyen Zurak da ke karamar Wase a jihar Filato
- Wani basaraken gargajiya da ya halarci jana'izar mutanen, Lawal Idris ya tabbatar wa manema labarai samun karin gawarwaki
- Lawal Idris ya kuma bayyana halin da mutanen garin ke ciki biyo bayan zuwan sojojin Najeriya a ranar Talata da ta wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da yan bindiga suka kai Zurak a karamar hukumar Wase ta jihar Filato ya karu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an samu karin mutane shida da suka mutu cikin wadanda da suka samu raunuka.
A lokacin da yan bindigar suka kai harin sun kashe mutane 50 tare da raunata mutane da dama da kona gidaje masu yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya jawo mutanen garin suka gudu zuwa garuruwan da ke kusa da su domin neman mafita da matsuguni.
Zurak: Basarake ya yi karin haske
Wani basrake mai suna Lawal Idris ya shaida cewa ya halarci jana'izar mutane 50 da aka kashe a karon farko ya kuma ce an kara samun karin gawarwaki.
Ya ce bayan an gama jana'izar mutane 50 din an kara samun mutane shida da suka mutu kuma dukkansu maza ne.
Meya faru bayan zuwan soji Zurak?
Basaraken ya tabbatar wa manema labarai cewa bayan zuwan sojoji ranar Talata mutanen da suka gudu sun dawo gidajensu.
Ya kara da cewa zuwan sojojin ya kwantar wa mutane hankali kuma za su cigaba da zama a garin karkashin kulawar jami'an sojin.
Za a canza kasuwar shanu a Jos
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar masu sayar da shanu a jihar Filato ta koka kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na canza musu kasuwa da suke hada hada.
Gwamnatin jihar ta ba su wa'adin mako biyu domin su su tashi daga kasuwar Kara da ke Bukuru amma yan kasuwar sun koka kan rashin tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng