An Tsure Bayan Dattijo Mai Shekaru 70 Ya Mutu a Cikin Kotu Yayin Ba da Shaida

An Tsure Bayan Dattijo Mai Shekaru 70 Ya Mutu a Cikin Kotu Yayin Ba da Shaida

  • Wani dattijo mai shekaru 70 ya rasa ransa a cikin kotu yayin da ya je shi domin ba da shaida a jihar Ondo
  • Lamarin ya faru ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu a babbar kotun jihar da ke Oka yayin shari'a a kotun
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar haka a yau Laraba 22 ga watan Mayu inda ta ce sun dauki gawar dattijon

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - An shiga fargaba bayan wani dattijo ya fadi ya mutu a cikin kotu ana daf da fara gudanar da shari'a.

An kira dattijon mai shekaru 70 kotun da ke jihar Ondo ne domin ya ba da shaida kan wata rigima.

Kara karanta wannan

'Banex Plaza': Soja ya shararawa wata mata mari har ta fada doguwar suma

Wani dattijo ya mutu ana shirin fara shari'a a cikin kotu
Dattijo mai shekaru 70 ya mutu bayan ya shiga kotu ba da shaida. Hoto: Court of Appeal.
Asali: UGC

Yaushe dattijon ya mutu a kotu?

Lamarin ya faru ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu a babbar kotun jihar da ke Oka kafin fara shari'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta tabbatar da cewa dattijon ya zo kotun ne domin ba da shaida kan wata shari'a da ake yi da abokinsa.

Wani ma'aikacin kotun ya ce dattijon da ba a bayyana sunansa ba ya fadi ne ba tare da wani abu ya faru tsakaninsa da wani ba, cewar Tribune.

"Dattijon yana kotu inda ya je ba da shaida da abokinsa, kawai ya fadi kasa inda ya buga kansa da siminti nan take ya mutu."
"Bai yi kama da wanda za a ce ba shi da lafiya ba, kuma bai yi wata rigima da wani ba da za a ce shi ne dalilin mutuwarsa."

Kara karanta wannan

'Dan Tik Tok ya kashe kansa bisa kuskure a idon mabiyansa wajen yin bidiyo

- Ma'aikacin kotun

Ƴan sanda sun dauki gawar dattijon

Wani shaidan gani da ido, Tunde Ariyon ya ce dakarun 'yan sanda Enu-Owa sun karaso kotun domin daukar gasar marigayin.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce za a gudanar da bincike a hedkwatar hukumar da ke Akure.

Kotu ta tube sarki a Ondo

Kun ji cewa babbar kotu ta tube rawanin basaraken Owo, Oba Michael Adetunji, daga mukamin Sarkin Ute a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

Oba Michael Adetunji Oluwole ya shiga takaddamar shari'a game da zamansa sarki tun a shekarar 1995.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.