Yadda 'Yan Daba Suka Hallaka Ma'aikacin Lafiya a Wajen Bikin Aure a Neja

Yadda 'Yan Daba Suka Hallaka Ma'aikacin Lafiya a Wajen Bikin Aure a Neja

  • An kashe wani ma’aikacin lafiya mai suna Umar Mohammed a wajen wani bikin aure a Unguwar Gbegenu da ke Minna a jihar Neja
  • Wasu ƴan daba ne suka cakawa Umar Mohammed wuƙa a kai, bayan sun kutsa wajen taron bikin auren
  • Jami’an ƴan sanda sun cafke mutum biyu da ake zargi yayin da suke ci gaba ƙoƙarin ganin sun cafke sauran waɗanda ake zargin da suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Minna, jihar Neja - Wasu ƴan daba sun hallaka wani ma’aikacin lafiya mai suna Umar Mohammed a wajen wani bikin aure a unguwar Gbegenu da ke Minna a jihar Neja.

An tattaro cewa Umar Mohammed ya yanke shawarar halartar bikin auren ne bayan ya dawo daga wurin aikinsa a ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da jariri tare da mahaifiyarsa a jihar Kaduna

'Yan daba sun hallaka ma'aikacin lafiya a Neja
'Yan daba sun kashe ma'aikacin lafiya a jihar Neja Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan an garzaya da shi zuwa babban asibitin Minna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan daba suka tafka ɓarna

Jaridar The Punch ta rahoto cewa wani ganau ba jiyau ba, Haruna Aminu ya ce ƴan daban sun farmaki marigayin ne da mugayen makamai ƴan mintuna kaɗan bayan ya isa wurin bikin auren.

"Ba a dauki lokaci mai tsawo ba bayan ya isa wurin sai ƴan daban waɗanda adadinsu ya haura goma suka fara ihu da babbar murya. Sun riƙa ɗaga muggan makamai. Mutane da dama sun kauce sun ba su hanya yayin da wasu suka jikkata."
"Umar yana ƙoƙarin barin wurin bikin auren ne lokacin da ƴan daban suka bi shi, kwatsam sai ɗaya daga cikinsu ya daɓa masa wuƙa a kai. Nan take ya faɗi ƙasa jini na fita daga kansa."

Kara karanta wannan

Basarake ya faɗi yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 50, an yi masu jana'iza a Arewa

- Haruna Aminu

Me ƴan sanda suka ce kan kisan?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce an kama wasu mutum biyu da ake zargi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

"An tura tawagar jami'an sintiri na ƴan sanda zuwa wurin da lamarin ya auku kuma an cafke mutum biyu da ake zargi yayin da sauran suka tsere.
Ana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran waɗanɗa ake zargi yayin da ake ci gaba da bincike."

- Abiodun Wasiu

Magance matsalar ƴan daba a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya sanya dokar ta ɓaci kan munanan ayyukan ƴan daba a jihar.

Gwamnan ya umarci dukkan jami’an tsaro da su ɗauki mummunan mataki kan duk waɗanda ke neman ta da zaune tsaye a faɗin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel