'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Jariri Tare da Mahaifiyarsa a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Jariri Tare da Mahaifiyarsa a Kaduna

  • Wani jariri mai kwana bakwai a duniya tare da mahaifiyarsa sun faɗa hannun ƴan bindiga bayan sun tare motarsu a kan hanya
  • Ƴan bindigan sun sace su ne tare da wasu mata huɗu da direbansu yayin da suke kan hanyar dawowa daga kasuwa a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna
  • Miyagun sun tuntuɓi iyalan mutanen da suka sace inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 25 a matsayin kuɗin fansa kafin su sake su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da jaririnta wanda yake da kwana bakwai a duniya a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun sace su ne tare da wasu mata huɗu da direbansu yayin da suke dawowa daga kasuwar Jere zuwa ƙauyen Dodon-Daji da ke ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Basarake ya faɗi yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 50, an yi masu jana'iza a Arewa

'Yan bindiga sun sace jariri a Kaduna
'Yan bindiga sun sace mutum bakwai a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce wani mazaunin garin Kagarko mai suna Suleiman Musa ya shaida mata ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:12 na daren ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙauyen Dogon-Daji yana da nisan kilomita ɗaya daga garin Kagarko a Kaduna.

Yadda ƴan bindiga suka sace mutanen

Ya ce matan sun je sayar da kayan amfanin gona ne a kasuwar Jere sannan suna kan hanyar dawowa a cikin wata mota ƙirar Golf sai kwatsam ƴan bindiga suka fito daga daji suka buɗe wuta kan tayoyin motar. 

"Ba zato ba tsammani sai ƴan bindigan suka fito daga cikin daji sannan suka harbi tayoyin motar, lamarin da ya sanya dole direban motar ya tsaya, hakan ya sanya suka yi awon gaba da matan tare da direban zuwa cikin daji."

- Suleiman Musa

A cewarsa ƴan bindigan sun tuntuɓi iyalan mutanen da aka sace inda suka nemi a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 25.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7, sun kwato makamai masu yawa a Kaduna

Lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, SP Hassan Mansur, domin tabbatar da aukuwar lamarin, bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba.

Ƴan sanda sun hallaka ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa jami'anta sun kashe wasu ƴan bindiga mutum biyu.

Jami'an rundunar ƴan sandan sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu a hannun ƴan bindigan masu addabar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel