Hanyar da za a bi a shawo kan matsalar bara a Najeriya - Cise Dahiru Bauchi
- Yaron fitattacen malamin darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana yada za a iya shawo matsalar bara a Najeriya
- Sheikh Sidi Ali Cisse Dahiru Bauchi ya ce har wadanda ba almajirai ba sun zama masu bara saboda halin da kasar ke ci
Sheikh Sidi Ali Cisse Dahiru Bauchi, yaron fitattaccen malamin addninin musulunci na darikar Tijjaniyya, wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi,
Sidi Cise ya taba rike mukamin shugaban hukumar kula da makarantun Allo (Tsangaya) na jihar Bauchi, kuma shi ne shugaban harkokin ilimin makarantun mahaifin sa Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
A zantawar yayi da manema labarun, shehin Malamin ya fayyace dalilan yin almajiranci da yadda za a inganta almajiranci ta yadda almajirai za su daina yin bara da kansu a kasar.
Mallamin yace almajirancin ya zama har wadanda ba almajirai ba, sun zama almajirai, kowa ya zama almajiri saboda halin da kasar take ciki a yanzu.
KU KARANTA : An bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mukamin sa na ministan mai
Idan gwamnati ta yi da gaske kuma al’umma suka tsaya akan tsoron Allah, tabbas an dauko hanyar yin maganin bara a kasar.
Saboda yawanci abubuwan batanci da ake ganin almajirai ne yi, gaskiya almajirai ba ne wasu ne suke shiga cikin rigar almajiranci suna barna.
Yawancin masu bara ba almajiranci ya sa su ba, tsananin talauci da maraici da rashin gata da matsalolin yau da kullum suka sa mutane da yawa barace-barace ake dora laifin barar da suke yi a kan almajiran da ke neman ilimin Alkur’ani.
Amma idan gwamnati za ta ingata makaratu da rayuwar mutanen Najeriya matsalar barace-barace zai zo karshe a Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng