Tsadar Rayuwa: Kwanaki Bayan Samun Mukami, Tsohon Gwamna Ya Kare Tinubu

Tsadar Rayuwa: Kwanaki Bayan Samun Mukami, Tsohon Gwamna Ya Kare Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kuncin rayuwa da ake ciki a yau
  • Malam Isa Yuguda ya ce shugaban kasar shi ma a haka ya samu Najeriya cikin rudanin tattalin arziki da rashin daidaiton al'amura
  • Har ila yau, ya kuma bayyana yadda cire tallafin man fetur ya jawo amfani ga Najeriya maimakon yadda wasu ke sukan matakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsin rayuwa da Najeriya ke ciki.

Isa yuguda
Isa Yuguda ya ce bai kamata a zargi Tinubu kan wahalar rayuwa ba. Hoto: Isa Yuguda
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya yi maganganun ne wajen wani taro da tsagin jam'iyyar APC ya shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Arewa guda 5 da Bola Tinubu ya ba manyan mukamai a jami'o'i

Malam Isa Yuguda ya ce bai kamata a zargi shugaba Tinubu kan jawo tashin farashin kayyakki da sauran wahalhalun da yan Najeriya ke fama da su ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene ya jawo tsadar rayuwa a Najeriya?

Duk da wahalhalun rayuwa da yan Najeriya suka shiga a mulkin Tinubu, Malam Isa Yuguda ya ce shugaban kasar shima gadonsu ya yi.

Ya ce tattalin arzikin kasar ya tabarbare tun kafin zuwan shugaba Bola Tinubu saboda haka bai kamata a zarge shi ba.

Kokarin Tinubu wajen kawo gyara

Malam Isa Yuguda ya kara da cewa shugaba Bola Tinubu ya dauki matakan da suka dace wajen kawo cigaban tattalin Najeriya.

Tsohon ministan ya ce ba don Tinubu ya dauki matakin cire tallafin man fetur da Naira ba, da yanzu kasar ta kai ga durkushewa.

Tinubu ya kyauta kan cire tallafin mai

Kara karanta wannan

An soki yadda Bola Tinubu ya kare shekaran farko a kan mulkin Najeriya

Tsohon gwamnan ya ce duk da cewa ba Tinubu ba ne ya fara cire tallafi man fetur amma hakan ya jawo amfani ga Najeriya.

Ya ce man da ake amfani da shi a Najeriya ya ragu sosai saboda cire tallafi ya sa an daina satar man zuwa kasashen ketare.

A cewar Isa Yuguda, a yanzu man da ake amfani da shi a Najeriya ya ragu da kashi 50% saboda an daina sace shi zuwa waje.

Shugaba Tinubu ya raba kayan abinci

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika tarin kayan abinci ga gwamnatin jihar Zamfara a jiya Litinin, 20 ga watan Mayu.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya tabbatar da karbar kayan abincin tare da bayyana adadinsa da yadda za su raba shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel