Isa Yuguda da wasu 'yan takara 8 na hankoron maye gurbin kujerar Marigayi Sanata Ali Wakil - INEC

Isa Yuguda da wasu 'yan takara 8 na hankoron maye gurbin kujerar Marigayi Sanata Ali Wakil - INEC

A ranar Talatar da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa watau INEC reshen jihar Bauchi, ta bayar da sanarwar tantance 'yan takara 9 daga jam'iyyu daban-daban dake neman maye gurbin kujerar Sanata a zaben ranar 11 ga watan Agusta da za a gudanar.

Legit.ng ta fahimci cewa, an samu gurbin wannan kujera ne sakamakon rasuwar Mallam Ali Wakil, Sanata mai wakilcin jihar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa da ajali ya katse ma sa hanzari tun kimanin watannin biyar da suka gabata.

Hukumar ta INEC da sanadin kakakin ta na jihar Bauchi, Yahaya Muhammad, shine ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a cikin Bauchin Yakubu a ranar da ta gabata.

Marigayi Sanata Ali Wakil

Marigayi Sanata Ali Wakil

Kamar yadda shafin jaridar Daily Nigerian ya kalato wannan rahoto da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya, mun samu cewa akwai 'yan takara 9 dake hankoron maye gurbin Marigayi Wakil da lamarin ya kasance sai wani ya rasa wani kan samu.

KARANTA KUMA: Gwamna Dickson ya yabawa Musulmai bisa tabbatar da zaman lafiya a jihar Bayelsa

Mallam Yahaya ya jeranto 'yan takarar da hukumar INEC ta tantance tare da jam'iyyun su kamar haka:

Haruna Ayuba - ADC

Lawal Gumau - APC

Aminu Tukur - APP

Isa Yuguda - GPN

Usman Hassan - KP

Husseini Umar - NNPP

Usman Chaledi - PDC

Ladan Salihu - PDP da kuma;

Maryam Bargel - SDP

Dangane da shirye-shiryen aiwatar da wannan zabe, Muhammad ya bayyana cewa, hukumar ta tanadi ma'aikata 3500 da za gudanar da wannan zaben a wurare kada kuri'u 1,944 cikin kananan hukumomi 7 dake karkashin mazabar Kudancin Bauchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel