InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Kakakin Majalisa Ya Tafka Babban Rashi

InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Kakakin Majalisa Ya Tafka Babban Rashi

  • An shiga jimami bayan Allah SWT ya karbi rayuwar mahaifin kakakin Majalisar jihar Lagos, Hon. Mudashiru Obasa
  • Marigayin Pa Sulaimon Atanda Obasa ya rasu yana da shekaru 83 a duniya da safiyar yau Talata 21 ga watan Mayu
  • Sakataren kakakin Majalisar, Eromosele Ebhomele shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Kakakin Majalisar jihar Lagos, Hon. Mudashiru Obasa ya yi rashin mahaifinsa.

Marigayin mai suna Pa Suleimon Atanda Obasa ya rasu ne da safiyar yau Talata 21 ga watan Mayu a jihar Lagos.

Mahaifin kakakin Majalisar jihar Lagos ya rasu
Kakakin Majalisar jihar Lagos, Hon. Mudashiru Obasa ya rasa mahaifinsa. Hoto: Eromosele Ebhomele.
Asali: Original

Wanene marigayi Obasa a Lagos?

Atanda wanda ɗan kasuwa ne kuma shugaban al'umma kafin rasuwarsa, ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 83 a duniya.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Arewa guda 5 da Bola Tinubu ya ba manyan mukamai a jami'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren kakakin Majalisar, Eromosele Ebhomele ya tabbatarwa Legit.

Pa Obasa ya kasance fitaccen ɗan kasuwa a bangaren mai da kuma harkokin noma a yankin.

Marigayin ya taimakawa matasan yankinsa wurin basu yadda za su dogara da kansu tare da bunkasa tattalin arziki.

Lagos: Gudunmawar da ya bayar ga Musulunci

An tabbatar da cewa marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wurin bautar Allah madaukakin sarki da taimakon al'umma.

Suleimon ya shafe rayuwarsa wurin taimakon marasa karfi da marayu tare da riko da addinin Musulunci hannu bibbiyu.

Pa Atanda ya rasu ya bar mata da kuma yara hade da jikoki wanda ya haɗa da Hon. Mudashiru Obasa, kakakin Majalisar jihar Lagos.

Za a sanar da lokacin sallar jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya fadin abin da ya kamata Abba ya yi bayan harin masallaci a Kano

Barasake ya kwanta dama a Osun

Kun ji cewa an tafka babban rashi bayan rasuwar fitaccen Basarake a jihar Osun, Aderemi Adedapo bayan fama da jinya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar 18 ga watan Mayu a asibitin koyar na Jami'ar Obafemi Awolowo da ke jihar.

Gwamna Ademola Adeleke ga mika sakon ta'aziyya game da rasuwar marigayin inda ya ce tabbas jihar ta tafka babban rashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.