TotalEnergies Ya Juyawa Najeriya Baya Kan Aikin Dala Biliyan 6, an Zabi Kasar Angola
- Kamfanin mai na TotalEnergies ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi aiwatar da ayyukan dala biliyan 6 a kasar Angola maimakon Najeriya
- TotalEnergies ya bayyana cewa Najeriya ba ta da tabbas a wajen tsare-tsaren siyasa, wanda ke sa fargaba a zukatan masu zuba jari
- Game da dalilin zabar Angola, kamfanin ya ce kasar na tsaya wa kaifi daya a kan tsare-tsarenta, sabanin Najeriya mai yawan sauya dokoki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kigali, Rwanda - Rashin tabbas kan tsare-tsaren da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa ya jawo kamfanin mai na TotalEnergies ya karkatar da dala biliyan 6 na ayyukan makamashi zuwa Angola.
Babban shugaban gudanarwa (CEO) na TotalEnergies, Patrick Pouyanne, ya bayyana cewa Najeriya ce ta fi dacewa da aikin, amma Angola ta fi ta kyawawan tsare-tsare.
Pouyanne ya bayyana hakan ne ga mahalarta taron shugabanin kamfanoni na Afirka a birnin Kigali na kasar Rwanda, a cewar rahoton BusinessDay.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TotalEnergies ya zabi Angola a kan Najeriya
Ya bayyana cewa Angola kasa ce mai tsayayyen tsarin siyasa, "wanda duk wani dan kasuwa zai fara la'akari da shi kafin fara zuba jari."
"Muna da kasashen da ke da ingantattun manufofi kamar Angola, ita kasa ce mai kaifi daya a kan tsare-tsarenta.
Don haka, mun zabi Angola kuma za mu fara aiwatar da manyan ayyuka na dala biliyan 6 a farkon makon nan domin a can suna tafiya ne da tsari tabbatacce."
Ko da yake shugaban na TotalEnergies ya ce yankin Neja-Delta shi ne ya fi samar da albarkatun mai a yammacin Afirka.
Jaridar SaharaReporters ta ruwaito shugaban yana cewa yanayin tsare-tsaren siyasar Najeriya ne ya ke zama cikas.
Matsalolin siyasar Najeriya da zuba jari
Pouyanne ya ce TotalEnergies ya shafe tsawon shekaru 12 ba tare da ya gudanar da aikin hakar mai a yankin ba, yana mai cewa "Najeriya na son tattaunawa kan harkalloli ba tare da an kai karshe ba."
Shugaban ya ci gaba da cewa:
“Kuna son yin muhawara a kan abu. A duk lokacin da aka samu sabuwar majalisa a Najeriya, to sai ta yi muhawara domin gyara ko bullo da sabuwar dokar man fetur.
"Idan ya zamana kasa ba ta da tabbas a kan tsare-tsaren siyasa, to yana da wahala ga masu zuba jari su narka kudi a inda ba su da tabbas kan me zai faru nan da dogon zamani."
Najeriya ta dukufa kan makamashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta dukufa wajen ganin ta karkatar da akalar ta daga dogara da man fetur zalla zuwa amfani da makamashi mai tsafta.
Wannan kuwa na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya aiwatar da wasu tsare da ayyuka a makon jiya da za su tabbatar da cewa kasar ta dauki saiti a bangaren makamashin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng