Fasa bututu ya jawo kwararar mai a Yankin Neja Delta

Fasa bututu ya jawo kwararar mai a Yankin Neja Delta

- Tsagerun Neja Delta sun fasa wani babban bututun man fetur na Kasar kwanaki

- Tsagerun na Neja-Delta sun fasa Bututun Forcados, hakan ya jawo mai ya kwarara cikin yankuna na Neja Delta kuma Kamfanin Shell na kokarin rage kwararar man

Fasa bututu ya jawo kwararar mai a Yankin Neja Delta
Bututun mai

 

 

 

 

 

 

Kwanakin baya wasu Tsagerun Neja-Delta suka fasa wani Babban bututun mai na Forcados da ake fitar da mai wajen Kasar nan domin a sayar. Sai dai fa baya ta zo da kura, don yanzu haka wannan aika-aika ya jawo babbar barna a Yankin nan na Neja-Delta.

Fashewar bututun ya sa mai ya kwarara kwarai a Yankin. Yanzu haka, man fetur ya shiga cikin ruwa da sauran Yankin na Neja-Delta saboda fashewar wannan babban bututu. Jaridar Punch tace wannan bututun ne yake fitar da mai wajen Kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai saki Nnmadi Kanu?

Bututun Forcados na Kamfanin Shell ne, yana Garin Burutu da ke Jihar Delta. A Ranar 9 ga Wata kuma Tsagerun na Neja-Delta suka fasa bututun. Wannan abu dai ya saka al’ummar Ogulagha cikin matsala. Man fetur ya kwarara zuwa cikin Garin da kuma cikin ruwa.

Yanzu haka dai Kamfanin Shell ta tura wasu Ma’aikatan ta domin kare kwararuwar man zuwa sauran wurare. Tsagerun Neja-Delta Avengers ne suka yi wannan barna ko can.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng