Fitaccen Basarake a Najeriya Ya Cire Tsoro, Ya Zargi EFCC da Karbar Rashawa

Fitaccen Basarake a Najeriya Ya Cire Tsoro, Ya Zargi EFCC da Karbar Rashawa

  • Oba na Benin, Uku Akpolokpolo Ewuare II ya dira kan hukumar yaki da cin hanci ta EFCC inda ya ke zargin wasu jami'anta da karbar rashawa
  • Sarkin ya nuna damuwa kan yadda wasu jami'an hukumar ke gudanar da ayyukansu ba tare da bin ka'ida ba yayin bincike
  • Ya bayyana yadda ya so taimakon hukumar yayin binciken wasu daga fadarsa amma mai kula da binciken ta ba shi kunya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Fitaccen basarake, Oba na Benin, Uku Akpolokpolo Ewuare II ya zargi Hukumar EFCC da cin hanci a Najeriya.

Basaraken ya ce hukumar tana taimakawa cin hanci da rashawa madadin dakile ta a kasar.

Kara karanta wannan

Congo: An shiga fargaba yayin da aka yi yunkurin juyin mulki, an yaɗa bidiyon

Basarake ya zargi EFCC da karbar na goro a Najeriya
Oba na Benin, Ewuare II ya koka kan wasu ayyukan hukumar EFCC a Najeriya. Hoto: @mrexpo.
Asali: Twitter

Basarake ya zargi EFCC da cin hanci

Mai martaba Ewuare II ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin daraktan yankin Benin, Effa Okim a fadarsa a jiya Litinin 20 ga watan Mayu a cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ba da misalin yadda aka cafke wasu masu mukami a fadarsa kan zargin damfara inda aka tasa keyarsu zuwa ofishin hukumar da ke birnin Benin.

Mai sarautar ya ce wasu daga cikin jami'an sun share maganar zargin inda daga bisani suka sake su, Vanguard ta tattaro wannan.

Jawabin Sarkin Benin kan hukumar EFCC

"Muna son jan hankalinku kan wasu abubuwa da ba su kamata ba kan ayyukan da kuke yi."
"Duk yadda ka yi kokarin taimakawa daga fada abin zai ba ka kunya, saboda na samu labarin cewa suna sauraron wasu ɓangarori kuma da wanda ya fi biya."

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

"Kun sani ni an sanni da fadin gaskiya, dole mu yi magana saboda wasu abubuwa da ke faruwa a ayyukan hukumar."

- Sarki Ewuare II

Basaraken ya yabawa sabon shugaban EFCC

Sai dai basaraken ya ce sabon shugaban hukumar, Ola Olukoyede da aka nada ya dauko hanyar gyara ayyukanta.

Sarkin ya koka kan yadda ya yi kokarin taimakon hukumar yayin binciken amma bai samu hadin kai ba.

Ya ce har takarda ya tura ga tsohon shugaban EFCC da aka sauke amma yadda wata jami'a ta gudanar da hukuncin bai yi masa dadi ba.

Basarake ya rasu a Osun

A wani labarin, an ji cewa fitaccen basarake a jihar Osun, Aderemi Adedapo ya riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadi 19 ga watan Mayu.

Mai girma Gwamna Ademola Adeleke ya nuna alhini kan mutuwar basaraken inda ya ce an tafka babban rashi a jihar gaba daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.