Shirin Ba Dalibai Rance: Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Daliban da Za Su Amfana

Shirin Ba Dalibai Rance: Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Daliban da Za Su Amfana

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana ɗaliban da za su amfana da shirin da ta kawo na ba da rance ga ɗaliban da ke karatu a makarantun gaba da sakandire
  • Manajan daraktan asusun ba da lamuni na ilmi (NELFUND), Akintunde Sawyerr ya bayyana cewa ɗaliban makarantun gwamnati ne kawai za su amfana da shirin
  • A ranar Juma'a 24 ga watan Mayun 2024 ne dai za a ƙaddamar da fotal ɗin da ɗaliban za su nemi rancen kuɗaɗen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Manajan daraktan asusun ba da lamuni na ilmi na Najeriya (NELFUND), Akintunde Sawyerr, ya bayyana cewa aƙalla ɗalibai miliyan 1.2 za su amfana da shirin.

Akintunde Sawyerr ya bayyana cewa ɗaliban za su fito ne daga makarantun gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi na shirin haɗa kai, ƙungiya ta faɗi wanda ƴan Najeriya za su zaɓa a 2027

Daliban da za su amfani da shirin ba dalibai rance
Gwamnatin tarayya ta ce daliban makarantun gwamnatin tarayya ne za su amfani da shirin ba dalibai rance Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wasu ɗalibai za su amfana da shirin?

Da yake magana gabanin ƙaddamar da shafin neman lamunin a ranar Juma’a, ya bayyana cewa ɗaliban da suka yi rajista a manyan makarantun tarayya za su fara amfana da shirin a matakin farko, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi nuni da cewa ɗaliban za su kasance ne waɗanda makarantunsu suka kammala ɗora bayanansu domin amfana da shirin.

Shafin neman bashin dalibai zai fara aiki

Akintunde Sawyerr ya bayyana cewa masu neman lamunin za su iya fara amfani da shafin daga ranar Juma'a, 24 ga watan Mayun 2024, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Ya ce an sauƙaƙa tsarin neman lamunin ta yadda ɗaliban da ke karatu a makarantun gwamnatin tarayya za su samu damar neman cin gajiyar shirin.

A cewar Akintunde Sawyerr, shirin wani muhimmin bangare ne na ajandar sabunta fata ta gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya shirya zai tsamo sama da mutane 7,000 daga ƙangin rashin aikin yi

"Muna kira ga dukkan ɗaliban da ke makarantun tarayya da su yi amfani da wannan damar wajen samun tallafin kuɗi domin iliminsu."
"Dole ne masu nema dole ne su gabatar da bayansu da wuri-wuri domin tabbatar da yin aikin kan lokaci."

- Akintunde Sawyerr

Adawar ASUU da shirin ba ɗalibai rance

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman jami'a watau ASUU ta reshen jihar Bauchi, ta jaddada ƙudirinta na ƙin amincewa da ba ɗalibai bashi.

Ƙungiyar ta ASUU ta yi nuni da cewa maimakon a ba ɗaliban rancen kuɗi, kamata ya yi gwamnati ta ba su tallafin karatu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng