Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami’in Kwastam a Abuja

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami’in Kwastam a Abuja

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da jimi'in kwastam a anguwar Shagari da ke birnin tarayya Abuja a jiya Lahadi, 19 ga watan Mayu
  • Bayan kama jami'in kwastam din yan bindigar sunyi nasarar tafiya da matarsa da 'ya'yansa guda uku da wani kaninsa daya
  • Daga nan yan bindigar sun wuce yankin Dakwa domin aikata ayyukan ta'addanci amma sun fafata da jami'an tsaro kafin su gudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Da safiyar jiya Lahadi ne gungun yan bindiga suka yi garkuwa da mutane biyar a birnin tarayya Abuja.

Police Ig
Yan bindiga sun kai hari Abuja, sun sace jami'in kwastam. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutanen ne a yankin anguwar Shagari da ke Dei-Dei.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa 'yan banga ne suka sanar da jami'an tsaron birnin Abuja faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da 'yan bindiga suka kama

'Yan banga sun tabbatar da cewa yan bindigar sun zo yankin ne da yamma kuma suka nufi inda wani jami'in kwastam yake zaune.

Da zuwansu suka kama jami'in kwastam din tare da matarsa mai ciki da 'ya'yansa uku da kuma wani kaninsa suka tafi da su.

Mai ciki ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

Sai dai biyo bayan tafiya da jami'in kwastam din da ilayansa, yan bindigar sun sako matarsa cikin kankanin lokaci, rahoton All News.

Duk da ba a samu karin haske kan dalilin sako ta ba, alamu suna nuna cewa sun sake ta ne saboda tana da tsohon ciki.

Yan bindiga sun kai hari Dakwa

Daga Shagari masu garkuwa da mutanen suka wuce yankin Dakwa domin kama wani mutum amma cikin sa a ba su yi nasara ba.

Kara karanta wannan

An samu yamutsi bayan bata gari sun afkawa sojoji a Abuja

Wan mai sarautar gargajiya a yankin, Dakta Alhassan Musa ya shaidawa manema labarai cewa an yi musayar wuta tsakanin masu garkuwa da mutane da jami'an tsaro a yankin kafin su gudu.

An kama dan bindiga a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Chinaza Phillip bayan musayar wuta.

Rahoto ya nuna dakarun ƴan sanda sun yi gumurzu da mayaƙan Phillip kafin daga bisa su yi nasarar kama shi da kubutar da wani mutum ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel