InnalilLahi: Fitaccen Farfesa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Jami'ar Maiduguri
- Fitaccen Farfesa a Najeriya da ke koyarwa a Jami'ar Maiduguri a jihar Borno ya riga mu gidan gaskiya
- Marigayin Farfesa Mustapha Kokari ya rasu ne a jiya Asabar 19 ga watan Mayu bayan fama da jinya a birnin Maiduguri
- Tuni aka gudanar da sallar jana'izarsa da safiyar yau Lahadi 19 ga watan Mayu da misalin karfe 9:00 a birnin Maiduguri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - An shiga cikin jimami bayan mutuwar fitaccen Farfesa a Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno.
Marigayi Farfesa Mustapha Kokari da ke tsangayar halittu ya rasu ne a jiya Asabar 18 ga watan Mayu.
Yaushe marigayin ya rasu a Maiduguri?
Kokari wanda ya sha fama da jinya kafin rasuwarsa ya rike mukamai da dama a tsangayar da ke Jami'ar, Cewar YerwaExpress.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuni aka gudanar da sallar jana'iza wanda aka sanar da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Lahadi 19 ga watan Mayu.
Wata majiya ta sanar da mutuwar marigayin a jiya Asabar 18 ga watan Mayu.
"Inna lillahi wa inna lillahi raaji'un, cikin alhini da mika kai ga Ubangiji, ina mai bakin cikin sanar da mutuwar Farfesa Mustapha Kokari."
"Muna addu'ar Allah ya yi masa rahama, ya yafe masa kura-kuransa ya kuma ba shi aljanna firdausi, Ameen."
- Cewar majiyar
Babban ɗan marigayi Shehun Borno ya rasu
Har ila yau, An shiga jimami bayan sanar da rasuwar babban ɗan marigayi Shehun Borno, Shehu Mustapha Umar El-Kanemi.
Marigayin Alhaji Shehu Mustapha El-Kanemi ya rasu ne a daren jiya Asabar 27 ga watan Afrilu a jihar Borno.
Zulum ya tafka babban rashi a gwamnatinsa
A wani labarin, Gwamna Babagana Umara Zulum ya sanar da mutuwar hadiminsa na musamman a bangaren harkokin al'umma.
Marigayin Kester Ogualili ya rasu ne bayan fama da jinya a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno.
Ogualili wanda asalin ɗan jihar Anambra ne ya shafe mafi yawan shekarunsa a jihar Borno wanda ya rike mukamai a gwamnatocin jihar da dama.
Asali: Legit.ng