Hukumar EFCC Ta Mayarwa Amurka $22,000 da Wani Dan Najeriya Ya Sata Ta Yanar Gizo

Hukumar EFCC Ta Mayarwa Amurka $22,000 da Wani Dan Najeriya Ya Sata Ta Yanar Gizo

  • Hukumar EFCC ta mayarwa Amurka wasu kudaden da dan Najeriya ya yi damfararsu ta yanar gizo
  • An ruwaito yadda alkali ya yankewa damfara Hakeem hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru biyu
  • FBI ta yi martani mai daukar hankali kan yadda EFCC ya yi aikin da kuma alkawarin da ta dauka

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Legas - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta mayarwa hukumar tsaron Amurka ta FBI $22,000 da aka kwato a hannun wani dan damfarar yanar gizo, Hakeem Olanrewaju.

A rahoton da uka samu, an gurfanar da Hakem ne a kotu bisa zarginsa da aikata zamba cikin amince a kafar yanar gizo.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: EFCC za ta binciki 'dan majalisa kan daukan nauyin ta'addanci

Mai magana da yawn EFCC, Dele Oyewale ya fadi a ranar Asabar cewa, an mikawa FBI kudin ne a ranar Juma'a 17 ga watan Mayu.

Yadda EFCC ta mayar da kudin da dan Najeriya ya sace a Amurka
An mayarwa FBI kudin da dan Najeriya ya sata | Hoto: Economic and Financiak Crimes Commision
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za mu ci gaba da aikinmu na yaki da rashawa, EFCC

Ya kuma bayyana cewa, hukumar a shirye take wajen yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ta ci gaba da zakulo irin wadannan tare da mayarwa masu dukiyar hakkinsu, rahoton Channels Tv.

A lokacin da yake karbar kudin, wakilin FBI, Charles Smith ya yabawa EFCC bisa wannan babban aiki da kuma jajircewa wajen ganin bayan barna.

Ya kuma tabbatarwa EFCC cewa, FBI da ma Amurka za su ci gaba da alaka da kuma hada kai wajen yaki da rashawa.

Wanne hukunci aka yankewa Hakeem?

Idan baku manta ba, a ranar 15 ga watan Agustan 2023 ne mai shari'a Nicholas Owibo na kotun tarayya da ke Ikoyi a birnin Legas ya umarci a mayar da kudin da aka kwato a hannun Hakeem ga Amurka, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya kone masallata su na tsakar sallar asubahi a Kano

Hakazalika, ya dauki Hakeem tsawon shekaru biyu a gidan yari bisa kama shi da laifin zamba da damfara.

Akan kama matasan Najeriya da aikata laifukan da suka shafi rashawa da cin amana game da damfara ta yanar gizo.

An gano ana daukar nauyin ta'addanci ta Crypto

A wani labarin, hukumar EFCC ta bayyana cewa ‘yan ta’adda na amfani da Binance da sauran manhajojin cryptocurrency wajen samar da kudin da suke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce 'yan ta'addan na amfani da matasa da ke harkar crypto wajen hada-hadar kudin ba tare da sun san duhun garin ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Olukoyede ya yi magana ne a ranar Laraba a taron masu ruwa da tsaki kan yaki da safarar kudi domin daukar nauyin ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel