Bola Tinubu Ya Ba Farfesa Attahiru Jega Babban Mukami a Gwamnatin Tarayya

Bola Tinubu Ya Ba Farfesa Attahiru Jega Babban Mukami a Gwamnatin Tarayya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba Farfesa Attahiru Jega babban mukami a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto
  • Farfesa Attahiru Jega na cikin mutane 555 da shugaban kasar ya naɗa shuagabancin kwamitocin gudanarwa a manyan makarantu
  • Gwamnatin tarayya ba bayyana rana da wurin da za a yi bikin kaddamar da wadanda aka ba muƙamin domin fara gudanar da aiki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega babban mukami.

Farfesa Jega
Farfesa Jega ya zama shugaban kwamitin gudanarwar jami'ar Danfodiyo da ke Sokoto. Hoto: Elder Solomon Harry
Asali: Facebook

Farfesa Attahiru Jega wanda tsohon ma'aikacin jami'a ne, Bola Tinubu ya nada shi shugaban kwamitin gudanarwa a jami'a.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada tsofaffin gwamnoni 4 da Ministan Buhari a manyan muƙamai

Rahoton da jaridar Leadership ta wallafa ya nuna cewa Farfesa Jega na cikin mutane 555 da shugaban kasa ya ba mukamai a makarantun gaba da sakandare da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukamin da Tinubu ya ba Jega

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba Farfesa Jega shugaban kwamitin gudanarwa a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.

Sauran mambobin kwamitin da Farfesa Jega zai yi aiki da su sun hada da Mary Nyieor Yisa, R.O Kazeem, Farfesa Usman Musa da Dakta Anthony Usoro.

Yaushe Farfesa Jega zai fara aiki?

Za a kaddamar da Farfesa Jega da ma sauran mutane 555 da shugaba Bola Tinubu ya ba mukamai a jami'o'i cikin makonni biyu.

Ana sa ran yin bikin kaddamar da su a ranakun Alhamis da Juma'a, 30 da 31 ga watan Mayu a hedikwatar hukuma mai kula da jami'o'i ta kasa (NUC) a Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba tsohon Gwamnan Zamfara da sakataren gwamnatin 'Yaradua mukamai

ASUU: Nadin mukaman zai hana yajin aiki?

Masana na hasashen cewa mukaman da Bola Tinubu ya bayar a jami'o'i nada alaka da biyan bukatun kungiyar ASUU domin kaucewa tafiya yakin aiki.

A satin da ya wuce ne kungiyar ASUU ta ba shugaban kasar mako biyu domin biya mata bukatun ta guda tara cikin har da nada shugabannin gudanarwa na jami'o'i.

Jega ya bukaci yin gyara a INEC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega ya bukaci a sauya kundin tsarin mulki na nadin shugaban hukumar INEC.

Farfesa Jega ya bayyana haka ne yayin wani babban taro da ya halarta a jihar Akwa Ibom inda ya shawarci sauya dokar nadin shugaban hukumar da shugaban kasa ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng