Jega Ya Buƙaci Sanatoci Kada Su Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Ta Naɗin Onochie
- Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ya shawarci sanatoci da kada su amince da buƙatar Buhari
- Tshohon shugaban ya shawarci shugaban ƙasa ya maye gurbin Lauretta Onochie, da wata mace a jiharta
- Jega yace duk mutumin da naɗinsa kawai ya jawo irin wannan tada ƙura to zai iya jawo INEC ta rasa yardar da aka mata
Tsohon shugaban hukumar zaɓe, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga majalisar dattijai kada ta amince da naɗin Lauretta Onochie, a matsayin kwamishinan INEC, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: An Tabbatar da Ɓullar Sabuwar Cutar COVID19 Mai Kisa a Jihar Oyo
The cable ta rahoto cewa Onochie, wacce take cikin waɗanda shugaba Buhari ya aike da sunansu, tana daga cikin waɗanda sanatocin suka tantance ranar Alhamis.
Naɗin Onochie ya jawo cece-kuce daga ƙungiyoyi masu zaman kansu, yan majalisun jam'iyyun adawa da ma wasu yan jam'iyya mai mulki ta APC.
Mutane da dama na ganin bai kamata a naɗa yar siyasa dake ƙaunar wata jam'iyya a matsayin kwamishina ta babbar hukuma kamar INEC ba.
Da aka yi fira da shi a shirin 'Sunday Politics' na gidan talabijin ɗin channels tv, Jega yayi jawabi dangane da maganganun dake kai kawo a kan naɗin Onochie.
Yace: "Irin waɗannan cece-kucen abun gujewa ne, duk wanda zai jawo irin wannan tada ƙura, to masu alhakin naɗin su kula sosai saboda ba zaka so ka naɗa wanda zai jawo zargi da shakka ba, kuma hakan zai sa hukumar ta rasa yardar da ake mata."
Farfesa Jega ya ƙara da cewa ya kamata shugaban ƙasa ya janye sunanta, ya maye ta da wata mace daga jihar da ta fito.
Tura sakamakon zaɓe ta na'ura
Tsohon shugaban INEC ɗin ya yabawa yan majalisun tarayya bisa ƙoƙarin da suke na zartar da kudirin gyaran dokokin zabe, amma ya nuna rashin amincewarsa da sake tura sakamako ta na'ura wato ta yanar gizo.
KARANTA ANAN: Anga Wata a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Ranar da Musulmai Zasu Yi Eld-Eil Kabir 1442AH
Yace: "Ba zai yuwu ka amince INEC ta gudanar da zaɓe ta na'ura ba kuma kace ba za'a tura sakamakon ta wannan hanya ba, saboda suna tafiya ne kafaɗa da kafaɗa."
A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna
Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya tabbatar da mutuwar tsohon mataimakinsa , Barnabas Bala Bantex.
Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ɗan uwansa kuma abokin gwagwarmaya.
Asali: Legit.ng