Jama’a Sun Soki Shirin Tinubu Na Kashe Naira Tiriliyan 20 da Aka Ajiyewa ‘Yan Fansho

Jama’a Sun Soki Shirin Tinubu Na Kashe Naira Tiriliyan 20 da Aka Ajiyewa ‘Yan Fansho

  • Gwamnatin tarayya tana tunanin kashe kudin ‘yan fansho domin gina abubuwan more reayuwa a Najeriya
  • Wasu ba su gamsu da wannan yunkuri da aka fara tunanin aiwatarwa a zamanin shugaba Bola Tinubu ba
  • Ana ganin za a batar da dukiyar da aka yi wa tsofaffin ma’aikata tanadi ba tare da an yi aikin fari ko na baki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta nuna sha’awar amfani da kudin tsofaffin ma’aikata wajen yin ayyukan gina kasa.

Wannan batu da gwamnatin tarayya ta kinkimo ya jawo abin magana a Najeriya musamman a kafofin sada zumunta na zamani.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana son taba kudin fansho a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gwamnatin Tinubu da dukiyar fansho

Legit ta bibiyi abin da wasu suke fada a shafin X wanda aka fi sani da Twitter, ta duba ra’ayoyin al’umma a game da matsayar nan.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnoni da basu ga maciji da yaran gidansu bayan ɗarewa mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Injiniya Yusuf Tahir Adam ya na cikin wadanda suke adawa da yunkurin gwamnatin wanda Atiku Abubakar ya soka.

"Ina kwana, wannan tunatarwa ce cewa ka da kuyi amfani fanshonku. Za su lafta kudin kwangilolin kuma su sace kudi."
"Za su tatse kudin nan kuma su bar ‘ya ‘yanku da bashi da nauye-nauye, kuma ku yi ritaya daga aiki ba ku da komai."

- Injiniya Yusuf Tahir Adam

Jamilu Maiwada ya yi mamakin ganin yadda hankalin al’umma ya karkata daga batun, yake cewa an maida hankali a wasu abubuwa.

“Wai yan siyasa na kokarin sace mana fansho, amma ku fadan jinsi kuke yi.”
“Wallahi duk masu yin karya da shaidar zur da sunan SA zai ci uban shi ranar lahira.”
Kowa fa ya san yadda ake kwangila a kasar nan, sai ayi wannan lalatar da fanshonmu?

Kara karanta wannan

Kamfanin hada-hadar kudi na Nigeria ya tafka asarar Naira biliyan 11, an yi masa kutse

- Jamilu Maiwada

Wasu sun ce babu laifi taba fansho

Irinsu M. S Ingawa suna ganin kyawun manufar a kokarinsa na maidawa Sanata Shehu Sani martani bayan ya soki batun a shafinsa.

Injiniya M. S Ingawa ya yi karin haske da cewa gwamnatin tarayya za tayi wa dokar fansho kwaskwarima domin halatta taba kudin.

Hadimin ministan harkokin gidajen na tarayya ya ce za a amfana da kudin a maimakon a bar su a jiye ba tare da ana juya su ba.

Fansho: Hadimin Tinubu ya yi magana

Bayo Onanuga ya ce cibiyar IMPI ta yi wa Atiku Abubakar raddi bayan ya soki matsayar, ya yi wannan magana ne a shafin X.

Mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai ya yi wannan magana da Niyi Akinsiju ya yi a kokarin kare gwamnatin APC.

Shugaba Tinubu ya rabu da Ganduje

A bangaren siyasa, an ji labari cewa rade-radi na cewa fadar shugaban kasa ta fara kokarin sauke shugaban jam'iyya APC na kasa.

Ana tunanin an samu kwamitin da zai nemo sabon shugaban APC bayan Abdullahi Ganduje wanda bai dade yana rike da NWC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel