Hajjin 2024: Gwamnan Arewa Ya Bai Wa Mahajjata Tallafin Maƙudan Kuɗi Bayan An Yi Karin N1.9m

Hajjin 2024: Gwamnan Arewa Ya Bai Wa Mahajjata Tallafin Maƙudan Kuɗi Bayan An Yi Karin N1.9m

  • Gwamna Inuwa Yahaya ya amince da bai wa kowane mahajjaci tallafin N500,000 sakamakon ƙarin kuɗin hajjin 2024
  • Mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ya ce wannan matakin zai taimaka wajen ragewa alhazan raɗaɗin matsin tattalin arziki
  • A kwanakin baya hukumar NAHCON ta sanar da ƙarin N1.9m kan kowace kujerar hajji saboda tashin farashin musayar kuɗi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da Naira 500,000 a matsayin tallafi ga kowane ɗaya daga cikin mahajjatan jihar su 1,273.

Gwamna Yahaya ya ɗauki wannan matakin ne domin tallafawa mahajjatan jihar Gombe biyo bayan ƙarin kuɗin aikin hajjin bana da aka yi a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa matashi ɗan shekara 36 a babban muƙami, ya faɗi wasu kalamai

Muhammad Inuwa Yahaya.
Gwamna Yahaya ya tallafawa mahajjatan jihar Gombe Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnan ya amince da cire waɗannan kuɗin ne a wani mataki na agaza wa alhazan jihar Gombe biyo bayan ƙarin N1.9m da hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi.

Idan baku manta ba NAHCON ta umarci kowane maniyyaci a Najeriya ya garzaya ofishinta na jiharsa ya biya ƙarin N1.9m bayan kudin hajjin da suka biya tun farko.

A cewar hukumar, an samu wannan ƙarin a kudin aikin hajjin bana 2024 ne saboda hauhawar farashin musayar kuɗin Najeriya, rahoton Tribune Nigeria.

Gombe ta taimakawa mahajjata

Amma a sanarwar da kakakin gwamnan ya fitar, ya ce Gwamna Yahaya ya tallafawa kowane maniyyaci da N500,000 ne domin rage masu raɗaɗin matsin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen bincike a babban banki CBN, ya ɗauki mataki

"Gwamna Yahaya yana fatan wannan tallafi zai taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin bana cikin sauƙi ga daukacin alhazan jihar Gombe," in ji shi.

Tun farko, gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta ba da tallafin N90bn domin ragewa alhazan Najeriya tsadar kuɗin kujera.

NAHCON ta gargaɗi mahajjata

A wani rahoton kuma Yayin da ake shirye-shiryen aikin hajjin bana 2024, hukumar jin daɗin alhazai ta bankaɗo wata matsala da ta kunno kai

A wata sanarwa ranar Alhamis, NAHCON ta gargaɗi mahajjata su yi hattara da wasu ƴan damfara da ke neman su ƙara kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel