Hajjin 2024: Gwamna Ya Gwangwaje Maniyyata 2,682 da Kyautar $100
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ba da tallafin kudi ga maniyyatan jihar 2,682 da za su tashi zuwa Saudiyya
- Gwamnan ya ba da kyautar $100 ga kowane maniyyaci a jihar domin ragewa musu halin da suke ciki na tsadar rayuwa
- Sanata Bala ya bayyana haka ne yayin da yake jawabin bankwana a sansanin aikin hajjin Sultan Sa'ad Abubakar da ke Bauchi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed ya gwangwaje maniyyatan jihar Bauchi da kyautar makudan kuɗi.
Gwamnan ya ba dukkan maniyyatan jihar 2,682 kyautar $100 domin tallafa musu yayin da suke kasa mai tsarki.
Gwamna ya shawarci maniyyatan Bauchi
Bala ya bayyana haka ne yayin jawabin bankwana ga maniyyatan a sansanin aikin hajji na Sultan Sa'ad Abubakar da ke Bauchi a jiya Juma'a 17 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadun jihar Bauchi nagari dama Najeriya baki daya, cewar rahoton Leadership.
Ya hori maniyyatan da su dage da yi wa Najeriya addu'ar zaman lafiya da kuma ci gaba a halin da ake ciki, kamar yadda Tribune ta tattaro.
Shirin da gwamnan ya yiwa maniyyatan Bauchi
Tsohon ministan ya ce sun yi dukkan mai yiwuwa wurin shirya tarbar maniyyatan karkashin jagorancin Amirul Hajji kuma Sarkin Dass, Usman Bilyaminu.
A martaninsa, Amirul Hajji, Usman Bilyaminu ya yabawa gwamnan kan irin shirye-shiryen da aka yi domin gudanar da aikin hajji cikin sauki da kuma walwala.
Sarkin ya kuma godewa gwamnan kan muƙamin da ya ba shi inda ya ce zai yi kokari wurin inganta harkokin aikin Hajjin bana.
Tinubu ya saka tallafi a aikin hajji
A wani labarin kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba da tallafin N90bn a aikin hajjin bana yayin da kujera ta yi tsada.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ya bayyana haka inda ya ce tallafin zai taimaka wurin ragewa maniyyatan wahala.
Shettima ya ce shugaban ya himmatu wurin inganta tattalin arzikin Najeriya domin samun daidaito a kasar.
Asali: Legit.ng