An Yi Garkuwa da Babban Malamin Addini a Nigeria, ’Yan Sanda Sun Magantu

An Yi Garkuwa da Babban Malamin Addini a Nigeria, ’Yan Sanda Sun Magantu

  • 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban malamin addinin Kirista a jihar Anambra, inda aka bazama neman su ba tare da nasara ba
  • Shugaban cocin Katolika na Onitsha, Prudentius Aroh, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa an dukufa yin addu’a domin ceto malamin
  • Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da sace limamin tare da yin karin bayani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Anambra - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Basil Chukwuemeka, wani babban limamin cocin Katolika a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Nigeria.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addinin Kirista
‘Yan sanda sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun sace malamin addinin. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda aka sace limamin Katolikan

Kamar yadda jaridar PremiumTimes ta ruwaito, an sace limamin cocin ne a ranar Laraba a Eke Nkpor ta Obosi da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban cocin na Katolika na garin Onitsha, Prudentius Aroh ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayun 2024.

Ya yi nuni da cewa shugaban limamai, Valerian Okeke, ya nemi mabiya darikar Katolika da su dage da yin addu’o'i domin a kubutar malamin, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

‘Yan sanda sun fara farautar miyagun

Sai dai rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta ce ta kaddamar da farautar wadanda suka yi garkuwa da malamin addinin tare da fatan kubutar da Fr. Gbuzue, rahoton jaridar The Sun.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, kakakin ‘yan sanda a jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nnaghe Obono Itam, ya yi jawabi ga limaman cocin Katolika yayin ganawarsu a Onitsha.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Benue, sun halaka mace mai juna 2 da wasu mutane 10

Kwamishinan ya kawar da fargabar da suke da ita tare da ba su tabbacin cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa domin ceto limamin, tare da kamo masu garkuwar.

'Yan sandan jihohi: Ina aka kwana?

A wani labarin, mun ruwaito cewa shirin kafa 'yan sandan jihohi ya samu karbuwa a wajen shugabannin majalisun jihohi 36 na Najeriya.

A halin yanzu, majalisar dattawa da ta wakilai na kara zage damtse domin ganin ta zartar da kudurin kafa 'yan sandan, yayin da tuni shugaban kasa da gwamnoni suka ba da goyon baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.