Niger: An Kama Yara 15 Cikin Mutane 30 da Ke Hakar Ma’adanai Ta Haramtacciyar Hanya

Niger: An Kama Yara 15 Cikin Mutane 30 da Ke Hakar Ma’adanai Ta Haramtacciyar Hanya

  • Gwamnatin jihar Niger ta cafke wasu mutane 30 bisa zargin hakar ma’adanan kasa ba tare da sahalewar gwamnati ba
  • Daga wadanda aka kama akwai maza 12 da mata 18, wanda mutane 15 daga cikinsu yara ne masu karancin shekaru, lamarin da ke jefa rayuwarsu cikin hadari
  • Darakta a ma’aikatar ma’adanan kasar jihar, Adamu Garba shi ne ya jagoranci sumamen da aka kai yankin Maitumbi inda ake hakar ma’adanan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Niger - Ma’aikatar ma’adanan kasa ta jihar Niger ta damke wasu mutane 30 da ake zargi da hakar ma’adanai a yankin Maitumbi ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Daga wadanda aka kama, 12 maza ne, wanda takwas daga cikinsu na da karancin shekaru, da kuma mata 18, wanda bakwai daga cikinsu masu karancin shekaru ne.

Gwamna Umar Bago
An kama mutane 30 da ke hakar ma'adanan kasa a Niger Hoto: Umar Bago
Asali: Facebook

Gwamnati ta mamayi masu satar ma'adanai

This day ta tattaro cewa wani darakta a ma’aikatar ma’adanan kasar jihar, Adamu Garba ya ce sun kai sumamen bazata ne yankin domin dakile ayyukan da ake yi ba tare da an nemi sahalewar gwamnati ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darakta a ma’aikatar ma’adanan kasar jihar, Adamu Garba ya ce daya daga dalilan kama wasu mutum 30 shi ne jaddada matsayarta na kakkabe hakar ma’adanai barkatai a jihar.

Ma'adanai: Ana samun 'yan kasar waje

Ya ce abin takaicin ne matuka yadda ake amfani da yara kanana wajen hakar ma’adanai duk da hadarin da hakan ya kunsa.

Ko a makon nan da mu ke ciki, ita ma gwamnatin jihar Oyo ta cafke wasu ‘yan kasar Sin biyu, da wasu mutum 30 da laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, kamar yadda Punch ta wallafa.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya kone masallata su na tsakar sallar asubahi a Kano

Darakata janar na rundunar Burst, Kanal James Oladipo Ajibolane ya sanar da hakan ga manema labarai, inda ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba.

Za a inganta tsaro a Niger

Mun ba ku labarin cewa dan majalisar wakilan Najeriya na duba yiwuwar samar da jami’an tsaro na musamman domin yaki da rashin taro da ya yi katutu a jihar Niger.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kara samun yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane, wanda ke salwantar da rayukan al’umar jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.