Hatsari ba sai a mota ba: Yadda wasu masu hakar ma’adanan kasa suka mutu yayin da kasa ta rufta dasu
Rundunar Yansandan jihar Filato ta sanar da mutuwar mutane biyu dake hakar ma’adanan kasa a sakamakon rufatawa dasu da kasa ta yi a jihar Filato, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar 7 ga watan Afrilu, a karamar hukumar Wase, kamar yadda Kaakakin rundunar Yansandan jihar, ASP Term Tyopev ya tabbatar.
KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Na yi da-na-sanin soyayyar da muka yi tare da Timaya
Kaakakin yace: “Da misalin karfe 11 na dare ne ofishin shugaban Yansandan karamar hukumar Wase ta samu rahoton cewa kasa ta rufta da masu hakar ma’adanan kasa a karamar hukumar Wase, har yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.
“Wadanda suka mutu sun hada da Safianu Yinusa da ya fito daga kauyen Kangial, na karamar hukumar Dengi Kanam na jihar, sai kuma Usman Abdullahi daga kauyen Gwaram, yankin Bashar na karamar hukumar Wase.” Inji shi.
Sai dai yace a yanzu haka sun kaddamar da bincike don tabbatar da musabbabin faruwar lamarin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng