Yadda Abacha ya kashe Yar'aduwa ya kuma yi kokarin hallaka ni - Obasanjo

Yadda Abacha ya kashe Yar'aduwa ya kuma yi kokarin hallaka ni - Obasanjo

- Allurar guba aka yi wa Shehu Musa Yaradua

- An so ayi min amma naki yarda

- Abacha ya sha alwashin baza mu fito da rai ba

Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, ya ce tsohon shugaban mulkin soja Janar Abacha ne ya kashe Shehu Yaraduwa, ya kuma so ya kashe Abiola, sannan ya nemi shima ya hallaka shi ta hanyar allurar guba, amma ubangiji ya cece shi.

Yadda Abacha ya kashe Yar'aduwa ya kuma yi kokarin hallaka ni - Obasanjo
Yadda Abacha ya kashe Yar'aduwa ya kuma yi kokarin hallaka ni - Obasanjo

A cewar Obasanjo, a jiya asabar, akwai muhimmin aiki da ya rage yayi wa Najeriya shi yasa Allah ya tserar dashi daga sharrin Abacha, wanda yace a salon mulkin Abachan ba adalci a ciki.

Ya kara da cewa, an ajje shi a wani gida a Legas watanni ukku, kain aka mayar dashi kurkuku da ke Jos. Amma da ya fara samun ziyara daga manyan kasa da shuwagabannin duniya, sai aka kai shi Yola aka boye a muguwar kurkuku.

KU KARANTA KUMA: Dubi hotunan tubabbun Yan Boko Haram da yadda gwamnati ke karrama su

A haka dai ya sha zama, inda wata rana wani likita yazo wai zai duba jininsa yayi masa allura ya bashi magani, shi kuwa yace atafau baza'a taba shi ba, garau yake.

'Hakan shi ne ya sa na tsallake amma nasan wannan itace allurar da aka yi wa Shehu aka zuba masa guba a jini, wadda ta halaka shi.' Obasanjon ya fadi.

Obasanjo ya kara da cewa, a lokutan da aka kama shi, yasha tunanin shi tashi ta kare, inda ya ke mamakin yadda ya bautawa kasa a ce a haka zai tai a banza, amma daga baya sai ya ga ai ba Najeriya ce ta wulakanta shi ba, mutum daya ne kacal.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng