Hisbah Kano: Jerin Muhimman Ayyuka 5 da Aminu Daurawa Ya Aiwatar Cikin Watanni 8

Hisbah Kano: Jerin Muhimman Ayyuka 5 da Aminu Daurawa Ya Aiwatar Cikin Watanni 8

Kano - Shugaban Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ɗauko wasu muhimman ayyukan gyaran tarbiya bayan sake naɗa shi kusan watanni 8 da suka wuce.

A ƴan kwanakin nan dai fitaccen malamin ya samu saɓani da Gwamna Abba Kabir Yusuf amma a ƙarshe an samu maslaha tsakaninsu ranar Litinin da daddare.

Sheikh Aminu Daurawa.
Hisbah Kano: Manyan Ayyukan da Sheikh Daurawa Ya Yi a Watanni 9 Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku wasu daga cikin manyan ayyukan da Daurawa ya fara bayan komawarsa Hisbah, ga su kamar haka:

1. Auren gata

Jim kaɗan bayan dawowarsa Hisbah, Sheikh Daurawa ya sanar da shirin gwamnatin Kano na ɗaukar nauyin ƙulla aure 1,000 a faɗin kananan hukumomi 44.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bayan fara shirin, Gwamnatin ta ƙara yawan ma'auran zuwa 1,800. Hisbah a ƙarƙashin Daurawa ce ta yi aikin tantancewa da duk wasu matakai har zuwa ranar ɗaura aure.

Kara karanta wannan

Majalisa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen ƴan bindiga a Jihar Arewa

Wasu daga cikin amaren auren gata.
Hisbah Kano: Manyan Ayyukan da Sheikh Daurawa Ya Yi a Watanni 9 Hoto: Kwankwason Tuwita
Asali: Twitter

Mafi akasarin waɗanda suka ci gajiyar auren gatan sun kasance zawarawa da matan da mazajensu suka mutu da kuma ƴan mata.

Gwamnatin Kano karkashin sabon gwamna, Abba Kabir Yusuf, ta biya sadakin N50,000 ga kowace amarya a madadin anguna, ta masu kayan daki da gara daidai gwargwado.

A lokacin Sheikh Daurawa ya buɗe ƙofar neman taimako daga attajirai kuma an samu waɗanda suka taimaka musamman wajen kayan garar da aka kai ɗakunan amare.

2. Operation Kauda Baɗala

Operation ‘Kau da Badala’ wani shiri ne na rundunar Hisbah karkashin Daurawa ta bullo da shi da niyyar yaki da fasikanci da tabbatar da tsafta kamar yadda Musulunci ya tanada.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan, kwamandan Hisbah ya ce sun kirkiro wannan Operation ne domin kawar da ayyukan baɗala a Otal-Otal, wurin cin abinci, wurin taruka da sauransu.

Jami'an hukumar Hisbah.
Hisbah Kano: Manyan Ayyukan da Sheikh Daurawa Ya Yi a Watanni 9 Hoto: Kano state Hisbah Board
Asali: Facebook

Ya ce kafin su je kowane irin aiki suna bin matakai, "farko idan aka kawo mana rahoton ana kaza a wuri kaza, muna tura ƴan Hisbah su je su tabbatar a farin kaya."

Kara karanta wannan

Kano: Jerin albishir 5 da Gwamna Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a zaman sulhu

"Amma idan sabon wuri ne aka buɗe, mu kan fara kiran masu wurin mu zaunar da su, mu karanta masu dokoki, idan ba su bi ba sai mu dira wurin."

Daurawa ya ƙara da cewa a yanzu Operation din ya yi sauki saboda an kulle musu asusu kuma suna ƙara horas da jami'ansu domin ci gaba da hana badala a Kano.

3. Natsar da ƴan Tiktok

Daga cikin ayyukan da Daurawa ya yi wanda ya ja hankali shi ne yunkurin natsar da masu amfani da manhajar Tiktok musamman irinsu Murja Kunya da sauransu.

Kwamandan ya fara gayyatar su zuwa ofishin Hisbah tare da yi musu nasiha kan su daina abubuwan da ba su dace ba, su rungumi kasuwanci.

Malamin ya ce a aljihunsa ya cire kuɗi ya ba su kuɗin Data da na mota kuma sun amsa gayyata. Waɗanda ba su ji nasiha ba kuma Hisbah ta ɗauki mataki a kansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe mutum 7 ƴan gida 1 da wasu bayin Allah

4. Tsaftace fina-finan Hausa

Bugu da ƙari, Daurawa ya zauna da masu sana'ar shirya fina-finan Hausa domin jan hankalinsu su gyara ayyukansu ya yi daidai da al'ada da addini.

Duk da jaruman Kannywood sun amsa gayyatar hukumar Hisbah amma wasu da dama ciki harda daraktoci da furodusoshi ba su je wannan taro ba.

A jawabinsa, Malam Daurawa ya nuna damuwarsan kan kwararar kananan yara a Kano da nufin shiga fim, inda suka kafa sansani suna aikata abubuwan da bai dace ba.

Ya kuma ja hankalinsu da su gyara wasu kura-kurai da suke yi a fina-finai kamar sanya tufafi da wasu kalamai da ka iya ɓata tarbiyar yara.

5. Yaƙi da barasa

Tun bayan komawarsa kan kujerar kwamandan Hisbah, Sheikh Daurawa ya sa ƙafar wando ɗaya da duk wasu ayyuka da suka shafi barasa, masu shigi da su da masu siya.

Ya kuma lashi takobin tsaftace jihar Kano daga barasa domin kawo karshen shaye-shaye da ɓata tarbiyyar yara masu tasowa da matasa.

Kara karanta wannan

UAE ta cire takunkumin hana 'yan Najeriya biza? Fadar shugaban kasa ta fadi gaskiya

Daurawa da Gwamna Abba sun sasanta

A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sun sasanta kuma ya koma kujerarsa ta kwamandan Hisbah.

Wannan ya biyo bayan wata ganawa da suka yi tare da manyan malaman Kano a gidan gwamnati da daren ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel