Gwamna a Najeriya Ya Tafka Babban Rashin Jigo a Gwamnatinsa, Ya Kaɗu Matuƙa
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa, Gboyega Soyannwo
- Sanwo-Olu ya bayyana rasuwar marigayin ne a yau Laraba 15 ga watan Mayu a shafinsa na X inda ya ce ya kadu da rasuwar
- Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin dan uwa ba wai ma'aikaci ba inda ya yi masa addu'ar samun rahama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Mataimakin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Legas, Gboyega Soyannwo ya kwanta dama.
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu shi ya tabbatar da mutuwar na hannun damansa a yau Laraba 15 ga watan Mayu.
Gwamna Sanwo-Olu ya kadu da mutuwar Gboyega
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Gbenga Omotosho ya fitar a yau Laraba 15 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Omotosho ya ce Soyannwo ya mutu ne a yau Laraba 15 ga watan Mayu bayan fama da jinya yana da shekaru 55 a duniya.
A cikin wata wallafa da gwamnan ya yi a shafinsa na X ya ce kadu da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa.
"Ina mai bakin cikin sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatana, Gboyega Soyannwo."
"Na kadu matuka da wannan mutuwa ta Gboyega da ta zo a bazata, wannan labari ya rikita ni."
- Babajide Sanwo-Olu
Lagos: Matsayin Gboyega a wurin Sanwo-Olu
Sanwo-Olu ya ce Gboyega ya kasance kamar ɗan uwa a gare shi ba wai mataimakin shugaban ma'aikatansa ba.
Ya ce gudunmawar da Gboyega ya bayar ba za a taba mantawa da ita ba a Lagos inda ya jajantawa iyalansa da ƴaƴansa kan wannan babbar rashi.
Zulum ya tafka babbar rashi
Kun ji cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya rasa hadiminsa, Cif Kester Ogualili a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.
Ogualili ya rasu ne a ranar 4 ga watan Mayun wannan shekara a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri bayan fama da jinya.
Marigayin wanda ya fito daga karamar hukumar Dunukofia a jihar Anambra ya shafe mafi yawan rayuwarsa a Borno.
Asali: Legit.ng