'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar

'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar

- Gwamnatin jihar Kaduna ta yi ƙarin haske game da jiragen sojoji masu saukan ungulu da ke yawo sararin samaniyar jihar

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya ce sojoji ne da ke yaƙi da ƴan bindiga ke sintiri

- Ya yi kira ga al'ummar jihar su kwantar da hankulansu kana suyi watsi da wadanda ke yaɗa jita-jita don tada hankulan al'umma

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce jirage masu saukan ungulu da ake gani suna shawagi a sararin samaniyar jihar farautar ƴan bindiga suke yi.

An samu hare-haren ƴan bindigan a wasu sassan jihar a watannin da suka gabata a Kaduna.

A wani harin baya bayan nan, a ƙalla mutum 12 aka ruwaito cewa sun rasu yayin wani hari a ƙauyukan Kidandan da Kadai a ƙaramar hukumar Giwa.

'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar
Taswirar Jihar Kaduna. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan kasuwa ya mika ƙorafi kan yadda DCP Abba Kyari ya 'tatsi' N41m daga hannunsa

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce mutane su kwantar da hankulansu "kan jiragen sojojin" don suna ƙoƙarin tsare mutanen jihar ne.

"Gwamnatin jihar Kaduna ta ce babu buƙatar mutane su tada hankulansu saboda jiragen sojojin da ke shawagi a sararin samaniyar Kaduna," inji sanarwar.

"Jiragen masu saukan ungulu da wasu jiragen jami'an tsaro ne da ke yaƙi da ƴan bindiga a wurare da dama a jihar.

"Gwamnatin ta bada wannan bayanin ga mazauna jihar da ke neman ganin zaman lafiya da doka da oda a jihar.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya ce maƙiyan Najeriya ne suka lalata zanga zangar EndSARs

"Gwamnatin Kaduna ta ce kada mutane su tada hankulan su game da jiragen saman sojojin da ke yawo a Kaduna," inji sanarwar.

Gwamnatin ta yi kira ga ƴan jihar su yi watsi da masu yaɗa labaran ƙarya kuma ta mika godiyar ta ga dukkan hukumomin tsaro da ke bada gudunmawarsu don samar da zaman lafiya a jihar.

A wani labarin, rundunar ƴan sanda ta jihar Ogun ta ce ta samu nasarar kama shahararren ɗan kungiyar asirin nan da ake nema ruwa a jallo, Akibu Tikare, a wurin da akayi fashi da makami a Ogijo, karamar hukumar Sagamu, Jihar Ogun.

Tikare, wanda ake zaton shine shugaban k'ungiyar asirin Eiye Confraternity, an kama shi ne a wani harin fashi da makami a tsakanin Gbaja da Kamalo a Ogijo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164