Gina Titin N30bn a Kano da Abubuwa 20 da Gwamnati Ta Amince da Su a Taron FEC

Gina Titin N30bn a Kano da Abubuwa 20 da Gwamnati Ta Amince da Su a Taron FEC

Abuja - A ranar Talata ne wani mai taimaka wa shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana muhimman ayyuka da tsare-tsare 20 da majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da su a taron ta na yini biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ayyukan sun haɗa da gina tituna da sayen motocin bas yayin da tsare-tsaren suka shafi wurare daban-daban da suka haɗa da gidaje, biza da kayan aikin zamani.

Wadannan ayyuka da tsare-tsare za su kara habaka tattalin arziki, da saukaka zuba jari da inganta saukin kasuwanci a kasar.

Gwamnatin tarayya ta kammala taron FEC na kwanaki biyu
Gwamnatin tarayya ta amince da ayyuka da tsare-tsare domin bunkasa tattalin arziki. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter
"Majalisar zartaswa ta tarayya ta kammala taronta da ta fara jiya (Talata), kuma majalisar ta amince da wasu ayyuka da tsare-tsare da za su bunkasa tattalin arziki."

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince gwamnati ta karbo bashin $500m a magance matsalar wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Mista Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

Jerin ayyuka da da tsare-tsare 20:

1. Samar da ababen more rayuwa da gidaje

Majalisar ta goyi bayan wasu tsare-tsare da za a kaddamar da za su domin kawo sauyi ga bangaren samar da ababen more rayuwa da gidaje a Najeriya ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da 'yan kasuwa.

Shirye-shiryen da za su iya samar da kusan Naira tiriliyan 2, za su canza fasalin ababen more rayuwa da sashin lamunin gidaje, da kuma samar da ayyukan yi.

2. Biyan kudin saukar jirage

FEC ta amince da cewa duk masu amfani da filayen jiragen sama na gwamnatin tarayya a duk fadin kasar za su rika biyan kudaden a saukar jiragensu.

Mun ruwaito cewa ba a ware kowa ba a wannan umarnin, domin hatta shugaban kasa da mataimakinsa za su rika biyan kudin idan jirginsu ya sauka.

Kara karanta wannan

Matar ɗan Sarkin Ingila, Harry ta ji dadin Najeriya, ta ce ta samu gida

3. An hana kwasar yashi kusa da gadoji

Majalisar ta sanar da haramta dibar yashi a tazarar kilomita 10 daga dukkanin gadojin gwamnatin tarayya a fadin kasar.

4. Garambawul ga bizar shiga Najeriya

Majalisar ta sanar da wa’adin makonni hudu domin sake duba tsarin ba da biza ga ‘yan yawon bude ido, ‘yan kasuwa da kwararru a fannin kirkira da ke son ziyartar Najeriya.

Wani ɓangare na garambawul din shi ne mazauna ketare na iya neman bizar a kan shafin intanet na gwamnati kuma su sami bizar cikin sa'o'i 48.

5. Tayar da jiragen da suka lalace

Majalisar ta amince da samar da kayan aiki, horar da ma’aikata kan yadda za a tayar da jiragen da suka lalace a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

Kwangilar dai za ta ci Naira biliyan 4.2.

6. Sayo motocin daukar kaya

Majalisar ta amince da sayo motocin SPV domin jigilar wayoyin intanet na tsawon kilomita 90,000 domin bunkasa karfin intanet na Najeriya da kashi 60 zuwa 70.

Kara karanta wannan

Tinubu ya haramtawa mukarraban gwamnati sayen motocin da suka dogara da fetur

7. Tsarin saka kudi a NITDA

Majalisar ta amince da biyan kudi domin a gudanar da nazari na yadda za a yi garambawul ga tsarin saka kudi ga hukumar NITDA.

8. Samar da cibiyar NDTEPH a Amurka

Majalisar ta amince da bukatar ma’aikatar sadarwa ta mayar da ginin gwamnati titin Jackson, San Francisco, Amurka zuwa cibiyar gudanar da shirin NDTEP.

9. Gina tashoshin bas

Majalisar zartarwa ta tarayya ta kuma amince da bayar da kwangilar gina tashoshin mota da sauran gine-ginen sufuri a babban birnin tarayya Abuja.

Dukkanin aikin zai ci Naira biliyan 51 kuma kamfanin Planet Projects Nigeria Limited ne zai aiwatar da shi.

10. Inganta titin Kwaita-Yebu, Abuja

Majalisar ta amince da bayar da kwangilar inganta titin Kwaita-Yebu da ke karamar hukumar Kuala a Abuja kan kudi Naira biliyan 7.6 ga kamfanin Messrs El & Matt Nigeria Limited.

11. Gina kotun daukaka kara a Abuja

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Majalisar ta amince da ba da kwangilar gina kotun daukaka kara ta Abuja kan kudi Naira biliyan 37.2. Kamfanin Messrs Visible Construction Limited ne zai aiwatar da aikin.

12. Saka fitulun titi kan hanyar Bill Clinton

Majalisar ta amince da ba da kwangilar saka fitulun titi a kan hanyar Bill Clinton, a babbar hanyar zuwa filin jiragen sama.

13. Sayo motoci 200 a kan N12.4bn

Majalisar ta amince da da bukatar da hukumar kwastam ta Najeriya ta yi na sayen mota kirar Toyota Land Cruiser Buffalo V6 guda 200 kan kudi Naira biliyan 12.5.

Gwamnati ta kuma amince da biyan inshorar motocin akan kudi Naira miliyan 522.

14. Hada dandalin karbar harajin caca

Gwamnati ta ba kamfanin Messrs Yuan Resources Limited ragamar hada dandalin tabbatar da karbar kudaden shiga ƙarƙashin tsarin PPP a ɓangaren caca da wasannin intanet.

15. Gina wasu tituna a fadin kasar

Kafin a dage taron na ranar Litinin zuwa ranar Talata, majalisar ta amince da wasu ayyukan hanyoyi. Daga cikin su akwai sake gina hanyar Iseyin-Okeho-Iganna a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta umarci CBN ya dakatar da karbar harajin tsaron yanar gizo

16. Sashi na 2 na babbar hanyar Legas-Calabar

Majalisar ta amince da sashe na 2 na ginin babbar hanyar Legas zuwa Calabar kan kudi naira tiriliyan 1.6.

17. Sake gina titin Koton-Karfe-Abaji

An amince da bayar da kwangilar sake gina hanyar Koton-Karfe-Abaji da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a jihar Kogi kan kudi Naira biliyan 89.

18. Daga darajar manyan tititunan Lokoja-Benin

A rana ta biyu na taron FEC, an amince da bayar da kwangilar daidaita hanyar Lokoja-Benin, da ya hada da sha tale-talen Okpela, da Auchi-Uromi.

Kamfanin simintin BUA ne zai dauki nauyin sake gina titin a kan kudi Naira biliyan 120 karkashin tsarin biyan haraji.

19. Gina tituna da gadoji a Kwara da Kebbi

Majalisar ta amince da ba da kwangilar gina tituna da gadoji ga ’yan kwangila daban-daban a Kaima-Tesse, jihar Kwara, Benin-Agbor, BeninByepass da Ngaski-Wara a jihar Kebbi.

Dukkanin wadannan kwangilolin guda hudu za su ci Naira biliyan 546.

Kara karanta wannan

N15tr: "Za mu binciki yadda aka ba da kwangilar titin Lagos-Calabar", Majalisa

20. Gina babban sha tale-tale a Kano

An ba kamfanin Messrs CCECC kwangilar gina babban sha tale-tale a jihar Kano a kan Naira biliyan 230.

Hanyar da ke da tsawon kilomita 37 za ta hada da gadojin kasa da kuma gadojojin sama da dama.

Gwamnati za ta siyo motocin CNG

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ba ta ma'aikatu, hukumomi da sassan gwamnati umarni da su sayo motocin da ke amfani da gas din CNG zalla.

A taron majalisar zartarwa, gwamnatin ta kuma haramtawa mukarraban gwamnatin sayo motocin da ke amfani da man fetur ko dizal.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel