Hukumar NYSC za ta Ware Masu Aikin Hidimar Kasa 5000, a Tallafa Masu da N10m

Hukumar NYSC za ta Ware Masu Aikin Hidimar Kasa 5000, a Tallafa Masu da N10m

  • Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin tallafawa masu hidimar kasa domin taimaka musu wajen dogaro da kai da samarwa wasu matasan ayyukan yi
  • Ministar matasa, Dr. Jamila Ibrahim da ta bayyana hakan ta ce za a rabawa matasan da ke hidimaar kasa 5000 kudi N10m domin bunkasa sana’arsu
  • Ta ce wannan na daga hanyoyin da gwamnati ke son bi wajen yiwa shirin NYSC garanbawul domin taimakawa matasa wanda zai taimaka wajen samar da aiki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana shirin tallafawa masu hidimar kasa domin samar da matasa masu sana’a maimakon dogaro da gwamnati.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Ministar matasa, Dr. Jamila Ibrahim ce ta bayyana hakan yayin taron farko na shugabannin hukumar kula da masu hidimar kasa ta NYSC, da sauran masu ruwa da tsaki a Abuja.

Dr. Jamila Ibrahim, Ministar Matasa
Gwamnatin tarayya za ta tallafawa matasa 5000 da jarin N10M Hoto: National Youth Service Corps - NYSC
Asali: Facebook

Ta bayyana cewa gwamnati na shirin tallafawa masu hidimar kasa 5000 da N10,000,000, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Jamila Ibrahim ta kara da cewa nan gaba ana sa ran hukumar za ta dinga yaye matasa masu sana’a da samarwa da Najeriya kudin shiga.

Za a kawo sauye sauye a NYSC

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa za a yiwa shirin hidimar kasa ta NYSC garanbawul domin kara inganta shirin.

Dr. Jamila Ibrahim ce da ta bayyana haka a Abuja ta ce gwamnati na son gina matasa da za su iya dogaro da kansu ta cikin shirin, kamar yadda Naija News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

A jawabinsa, Darakta Janar na hukumar NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed ya shaidawa shugabannin cibiyoyin dake samar da masu hidimar kasa cewa an shirya shirin ne domin karawa juna sani.

Ya ce sun gano wasu kalubale da ake fuskanta ciki har da rabawa masu hidimar kasar aiki, inda ya yi bayanin cewa za a samu sauki idan shugabannin wuraren aikin suna sanya ido.

An yankewa Minista hukunci kan NYSC

Mun kawo muku labarin cewa mai shari’a James Omotosho ya yanke hukunci kan karar da aka shigar gaban kotunsa ana neman tsige Hannatu Musawa daga mukaminta na Ministar Al’adu.

Mai shari’a James Omotosho ya ce babu isassun hujjojin da aka bayyana a gabanta da za su haramtawa Hannatu Musawa mukamin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada ta.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.