Bayan Kammala NYSC, Matashiyar Budurwa Ta Shilla Ƙasar Waje, Bidiyon Ta Ya Yaɗu

Bayan Kammala NYSC, Matashiyar Budurwa Ta Shilla Ƙasar Waje, Bidiyon Ta Ya Yaɗu

  • Wata budurwa ƴar Najeriya wacce ta kammala yiwa ƙasa hidima (NYSC) tabi sahun masu neman jaraba sa'ar su a ƙasashen waje
  • Bidiyon matashiyar ya ɗauki hankula bayan bayyanar hotunan ta cikin kayan NYSC da wasu kuma da ta ɗauka a ƙasar Ingila.
  • Mutane da dama a yanar gizo sun nuna mamakin su kan yadda matasa da yawa suke barin ƙasar nan

Wata matashiyar budurwa, @arikeonifoto, wacce ta kammala yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta sanya wani bidiyon ta a TikTok yayin da ta bar Najeriya ta koma ƙasar waje.

A farkon bidiyon matashiyar budurwar, an nuna ta a cikin sansanin wayar da kan masu yiwa ƙasa hidima cikin fararen kaya.

Budurwa
Bayan Kammala NYSC, Matashiyar Budurwa Ta Shilla Ƙasar Waje, Bidiyon Ta Ya Yaɗu Hoto: TikTok/@arikeonifoto
Asali: UGC

Can kuma kawai sai aka nuno ta sanye da cikakkun kayan masu yiwa ƙasa hidima, da farin hijabin ta a cikin bidiyon.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

Wasu hotunan ta sun nuno ta a filin jirgin sama da cikin wata mota sun tabbatar da cewa ta koma Ingila bayan ta kammala yiwa ƙasa hidima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama da suka yi sharhi a kan bidiyon ta sun, nuna mamakin su kan dalilin da ya sanya mutane da yawa ke yin bidiyo lokacin da za su fice daga ƙasar nan domin zuwa ƙasar waje.

Bidiyon ya yaɗu sosai

Bidiyon na ta ya yaɗu sosai, inda ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, sama da mutum 100 suka yi sharhi a kansa, yayin da sama da mutum dubu shida suka danna masa alamar so.

Ga kaɗan daga cikin sharhin da mutane suka yi akan bidiyon:

JAY GOLD ya rubuta:

"Mutane sai ficewa kawai suke daga ƙasar nan."

Kara karanta wannan

"Ke Gwana Ce" Bidiyon Yadda Wata Budurwa Mara Hannuwa Ke Sarrafa Ƙafafun Ta Ya Ɗauki Hankula

princewhyte401 ya rubuta:
"Ku na son ku bar ƙasar nan kawai a hannun Jagaban. Ina nan na adana waƙar."

Brownie_Gurrl ta rubuta:

"Na kalli sama da bidiyoyi 30 na barin ƙasar nan a cikin minti uku kacal. Haba ku yi haƙuri mana."

Bidiyon Ango Na Sharɓar Kuka a Wajen Ɗaurin Auren Sa Ya Ɗauki Hankula

A wani labarin kuma, bidiyon wani angon mai kuka a ranar ɗaurin auren sa ya ɗauki hankula sosai a yanar.

Kamar wani ƙaramin yaro kawai angon na amaryar sa sai kukaɓya kwace masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel