Kayayyaki Za Su Kara Tsada a Najeriya, an Kara Harajin Shigo da Kayan Kasar Waje
- An saka sabon fasalin harajin kwastam ga masu shigo da kaya don sahhale shigo da kayayyaki a tashoshin ruwan Najeriya
- Kwanan bayan nan ne farashin ya tafi daidai da yadda Naira ke tangal-tangal a hannun gwamnati da ‘yan kasuwar bayan fage
- Sabbin fasalin farashin na nufin shigo da kayayyaki kamar wayoyin hannu da motoci za su ci gaba da yin tsada ga ‘yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Babban bankin Najeriya (CBN) ya sake gyara fasalin farashin harajin shigo da kayayyaki zuwa Najeriya ta iyakokin ruwa da tudu.
Harajin na kwastam kudade ne da ake karba daga hannun masu shigo da kayayyakin waje kafin sahhale shigo da kayan da siyar dasu a Najeriya.
Ana biyan kudaden ne ta bankunan kasuwanci ga Hukumar Kwastam ta Najeriya, wacce ke karba a madadin gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda tsarin sabon kudin harajin shigo da kaya yake
Sabbin bayanai da aka buga a wata kafar kasuwancin gwamnatin tarayy sun nuna cewa masu shigo da kaya daga Najeriya za su siya dala akan N1,457/$.
Sabon farashin ya nuna karin kashi 2.99% daga yadda ya gabata a baya na N1,414.599 kan kowace dala a ranar Juma’a 10 ga Mayu, 2024.
Kaya za su kara tsada saboda harajin kwastam
A karkashin sabon umarnin babban bankin kasar, hukumar kwastam za ta kididdige kudaden da za ta karba ne bisa la’akari da sauyin farashin musayar kudi da aka samu.
Wannan gyara yana nufin masu shigo da kaya da suka cike ‘Form M’ a ranar Litinin, Mayu 13, 2024, za a caje su kan farashin da aka sabunta.
‘Form M’ tsari ne na tilas da ake cikawa ta yanar gizo don shigo da kaya na zahiri cikin kamar yadda hukumar kwastam ta tsara.
Gwamnati za ta ci bashin kudade daga kasar waje
A wani labarin, akwai yiwuwar Bankin Duniya ya amince da ba Najeriya rancen $2.25bn a ranar 13 ga Yuni, 2024 don yin wasu muhimman ayyuka guda biyu.
Wasu takardu daga hukumonin Najeriya sun nuna cewam za a raba kudaden da za a karbo ne tsakanin ayyukan don bunkasa tattalin arzikin Najeriya da karfafa tattara albarkatun kasa.
Daya daga cikin ayyukan da aka yiwa lakabi da REST zai mai da hankali ne ga yadda za a farfado da tattalin arzikin Najeriya da kawo sauye-sauye wajen samar da kudaden shiga, inda aka ce zai ci $1.5bn.
Asali: Legit.ng