Kashim Shettima Ya Bayyana Yadda Biyan Haraji Zai Amfani ’Yan Najeriya

Kashim Shettima Ya Bayyana Yadda Biyan Haraji Zai Amfani ’Yan Najeriya

  • Mataimakin shugaban kasa, sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa akwai alheri mai yawa kan tsarin karban haraji da gwamnati ta kawo
  • Sanata Kashim Shettima ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin da zai yi kwaskwarima kan kasafin kudi da karbar haraji a Najeriya
  • Ya kuma bayyana irin kokarin da kwamitin zai yi wurin tabbatar da har gwamnonin jihohi sun amfana da sakamakon da kwamitin zai fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, sanata Kashim Shettima ya bayyana yadda sababbin tsare-tsaren haraji da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo zai amfanar da Najeriya.

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa dukkan sababbin tsare-tsaren ana kawo su ne domin inganta rayuwar al'ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

Kashim Shettima
Kashim Shettima ya ce za a tabbatar ga an yi ayyukan da suka dace da harajin da aka tara. Hoto: Kashim Shettima.
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasan ya musanta zargin da wasu suke kan cewa harajin ba zai haifar da fa'ida ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Domin a cewarsa yanzu haka gwamnatin tana kan fito da shirye-shirye da za su tabbatar da cewa kowa ya ci moriyar harajin.

Wanda ya wakilci Kashim Shettima a taron

Rahotanni sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar ya yi jawabin ne ta bakin mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman, Dakta Aliyu Modibbo Umar.

Dakta Aliyu Modibbo Umar ya wakilci sanata Kashim Shettima ne a jiya Asabar a wani taron da kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan gyaran fuska ga kasafin kudi da haraji.

A cikin jawabin da ya gabatar, Dakta Aliyu Modibbo Umar ya ce halin da suka samu kasar a ciki ne ya saka shugaban kasa kirkiro sababbin tsare-tsare a kan haraji.

Kara karanta wannan

Harajin 0.5%: SERAP na shirin maka gwamnatin Bola Tinubu a kotu nan da kwana 2

Kashim Shettima ya yabi kwamitin karbar haraji

Yayin da yake bayyana ƙoƙarin da kwamitin suke, ya ce lalle akwai alama kan cewa suna kokari kuma tabbas za su ba maraɗa kunya.

A cewarsa, karin abin da ke nuna haka shine yadda kwamitin ya fara kokarin yadda za a aiwatar da shawarwarin da suka tattaro, cewar rahoton the Cable.

Kwamitin zai yi hadaka da gwamnoni

Ya kuma nuna cewa akwai tabbas wurin samun hadin kan gwamnonin jihohi wurin karban zartar da sakamakon da kwamitin zai fitar.

A karshe ya ce zasu tabbatar da samar da dukkan abin da ake bukata wurin ganin gwamnatoci sun yi aiki da natijar da kwamitin suka fitar.

Kashim Shettima ya magantu kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, sanata Kashim Shettima ya yi magana kan matsalar tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa idan ana son ganin an kawo ƙarshen matsalar dole ne sai an tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng