A Karshe, Ɗan Majalisar da Aka Ƙira Sunansa da Zargin Cin Hanci Daga Binance Ya Magantu

A Karshe, Ɗan Majalisar da Aka Ƙira Sunansa da Zargin Cin Hanci Daga Binance Ya Magantu

  • Dan Majalisar Tarayya, Dominic Okafor ya musanta zargin neman cin hanci daga kamfanin Binance da ake yi
  • Okafor ya ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya kan wannan labari da ake yadawa inda ya ce zai dauki matakin shari'a
  • Hakan ya biyo bayan zargin da shugaban kamfanin Binance ya yi na cewa wasu jami'an gwamnati sun nemi cin hancin $150m

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan Majalisar Tarayya da ake zargi da neman cin hanci daga kamfanin Binance ya yi martani kan lamarin.

Dominic Okafor daga jihar Anambra ya yi fatali da zargin inda ya ce babu kamshin gaskiya a ciki.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Dan Majalisa ya magantu kan zargin neman cin hancin $150m daga Binance
Dan Majalisar da ake zargi da neman cin hanci daga Binance ya yi martani. Hoto: @Ogundamisi, @officialEFCC.
Asali: Twitter

Matakin da Okafor zai dauka kan zargin

Okafor ya sha alwashin daukar matakin shari'a kan kafar sadarwa da ta yaɗa wannan zargi a kansa, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mamban Majalisar ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 10 ga watan Mayu yayin ganawa da manema labarai, Punch ta tattaro.

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin Binance ya zargi wasu jami'an gwamnati da neman cin hancin $150m domin kawar da tuhumar da ake yi wa kamfanin.

Okafor ya magantu kan zargin cin hanci

Sai dai Okafor ya ce an kawo maganar cin hancin ne domin kawar da hankulan jama'a kan kokarin da ya ke yi kan tuhumar kamfanin.

Ya ce yana daga cikin mambobin Majalisar da ke neman sai an gano musabbabin tserewar daya daga cikin shugabannin Binance, Nadeem Anjarwalla.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba yayin da 'yan banga suka bindige babban jami'in ɗan sanda a Taraba

"Jim kadan bayan gabatar da kudiri wanda ya samu karɓuwa, ana ta kira na ana yabamin kan haka, sai kuma aka fara kira na kan cewa na karbi cin hanci daga kamfanin."
"Na shiga damuwa matuka inda na rubuta takarda zuwa ga Premium Times wanda su ne suka fara yada labarin na karbi cin hancin."
"A takardar na bukace su da su janye wannan rubutu da suka yi cikin awanni 24 ko kuma na dauki matakin shari'a a kansu."

- Dominic Okafor

Majalisa ta yi martani kan cin hanci

A wani labarin, Majalisar Wakilai ta yi martani kan zargin neman cin hancin $150m daga kamfanin Binance kan matsalar da yake ciki.

Majalisar ta musanta haka inda ta ce an yi haka ne domin ɓata mata suna a kokarin binciken da take yi domin gano gaskiya kan zarge-zargen da ake yi wa kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.