Rundunar 'Yan Sanda za ta Ladabtar da Jami'in da Ya Nemi Jawo Abin Kunya a Titi

Rundunar 'Yan Sanda za ta Ladabtar da Jami'in da Ya Nemi Jawo Abin Kunya a Titi

  • Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta bayyana kama wani jami'inta bisa rashin nuna kwarewar aiki yayin sa-in-sa da wata direba
  • Wannan na zuwa ne bayan an gano wani jami'in 'yan sandan yana dukan wata direba Adelere Aisha da ta yi tukin ganganci
  • Rundunar ta bayyana cewa duk da jami'in nata ya yi kokarin tsayawa bisa doron aiki, amma an samu lamarin ya kwace masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta bayyana kama wani jami'inta bisa rashin nuna kwarewar aiki a wata dambarwa da wata direba, Aderele Aisha domin ladabtarwa.

Rundunar ta bayyana cewa duk da jami'in nata ya yi kokarin tsayawa bisa doron aiki, amma an samu lamarin ya kwace masa suka kusan kokawa.

Kara karanta wannan

'Yan Kalare: 'Yan sanda za su koyawa tubabbun tsageru sana'o'i a rage kashe wando

Aisha
Aisha ta sha mari a hannun jami'in 'dan sanda a Lagos Hoto: @rrslagos767
Asali: Twitter

Jawabin rundunar 'yan sanda a X

Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ana bukatar jami'in tsaro ya jajirce wajen nuna kwarewar aiki a kowane yanayi.

'Yan sanda sun ce fushi ya dauki jami'insu

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya ce jami'inta ya yi kokari lokacin da wata mai laifi ke kokarin cin zarafinsa.

Wani faifan bidiyo ya nuna wata direba, Aderele Aisha ta bi titi hannu daya, kuma ta dinga yiwa jami'in tsaron rashin kunya.

Leadership News ta ruwaito SP Benjamin Hundeyin na cewa duk da kokarin dakewa ya yi, sai da ya hau dokin zuciya har ya kusan bugunta.

Jami'in ya bayyana cewa tuni wacce ake zargi ta rubuta takardar neman afuwa kan yadda ta karya dokar hanya, da yiwa jami'inta rashin kunya.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

Ya kuma tunatar da al'umma muhimmancin su kasance masu da'a a mu'amalarsu da jami'an tsaro.

Kotu ta daure jami'in NSCDC

A baya kun ji cewa wata wani babban kwamandan hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC, Christopher Oluchukwu ya fuskanci fushin kotu bayan an kama shi da laifin zamba.

Ana zargin kwamandan da yaudarar wasu mutane uku tare da yi musu alkawarin samun aiki, inda kotun ta yi masa daurin shekaru biyar a gidan gyaran hali da tarbiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.