Sojoji Sun Mikawa Gwamnatin Borno Dalibar Chibok da Aka Ceto Bayan Shekaru 10
- Sojojin Najeriya da ke karkashin rundunar operation hadin kai sun mika dalibar Chibok da suka ceto ga gwamnatin jihar Borno
- A jiya Alhamis ne kwamandan rundunar ya jagoranci bikin mika dalibar, Lydia Simon tare da ƴaƴan da ta haifa a hannun Boko Haram
- Rundunar ta yi karin haske kan yadda suka ceto Lydia tare da bayyana matsayar su kan sauran daliban da suke jeji har yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar sojin operation hadin kai ta mika wata dalibar makarantar Chibok da suka ceto ga gwamnatin jihar Borno.
An mika dalibar mai suna Lydia Simon ga gwamnatin ne tare da 'ya'yan ta uku a jiya Alhamis, 9 ga watan Mayu.
Bayanan da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafin ta na Facebook, ya nuna cewa ceto ƴan makarantar Chibok lamari ne da ke nuna jajircewar sojojin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin kwamandan rundunar Sojoji
Kwamandan rundunar operation hadin kai, Manjo Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa sojojin sun yi matuƙar kokari wurin kutsawa maboyar ƴan Boko Haram domin ceto dalibar.
Manjo Janar Shaibu ta kara da cewa rundunar za ta cigaba da kokari wurin ceto raguwar ƴan matan da suke hannun ƴan kungiyar Boko Haram.
Yadda aka ceto dalibar Chibok
A yayin da yake bayyana yadda aka ceto dalibar, Birgediya Janar Abubakar Haruna ya tabbatar da cewa a karamar hukumar Gwoza aka ceto Lydia.
Sun ceto Lydia ne da ƴaƴan ta uku bayan sun kai farmaki kan 'yan Boko Haram a yankin Mandara a ranar 17 ga watan Afrilu.
Sojojin sun kuma kara da cewa an bawa Lydia da 'ya'yan ta uku kulawa ta musamman a asibiti domin tabbatar da lafiyarsu.
Sojoji sun gano gidan burodin ISWAP
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar ganowa tare da lalata gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.
Sojojin sun samu nasarar ne bayan shafe sama da mako guda suna fafatawa tare da ƴan ta'addan da suke kai hare-hare a yankuna da dama.
Asali: Legit.ng