Wutar Lantarki: Kamfanin KEDCO ya yiwa Abokan Huldarsa a Jihohi 3 Albishir

Wutar Lantarki: Kamfanin KEDCO ya yiwa Abokan Huldarsa a Jihohi 3 Albishir

  • Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki (KEDCO) ya yi albishir ga abokan huldarsa dake jihohin Arewa uku da cewa za a samu karuwar hasken wuta
  • Kamfanin ya ce zai samar da Karin 40MW na hasken wuta cikin watanni 18 a jihohin 3 na Kano da Jigawa da Katsina da kuma aiki, kuma yana aiki da gwamnoni
  • Haka kuma za a bullo da sabbabbin hanyoyin biyan kudin wuta domin dakile karkatar da kudin da ake kara daga abokan huldar kamfanin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki (KEDCO) ya yi albishir ga abokan huldarsa dake jihohin Kano, Jigawa da Katsina kan karuwar hasken wuta.

Kara karanta wannan

ICPC: Kotu ta daure jami'in tsaron NSCDC na tsawon shekaru 5 a kurkuku

Shugaban sashen hulda da jama’a na KEDCO, Sani Bala ne ya bayyana hakan, inda ya ce suna hada kai da wasu kamfanonin samar da makamashi domin bunkasa samar da hasken.

Kamfanin KEDCO
Kamfanin KEDCO ya ce za a samu karin hasken wuta a jihohi 3 na Arewa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A rahoton da Daily Trust ta wallafa, kamfanin zai samar da Karin 40MW na hasken wuta cikin watanni 18 a jihohin Kano, Katsina da Jigawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa wannan matakin na daga kokarinsu na wadata abokan huldarsu da hasken wutar duba da karuwar mutane a yankunan.

KEDCO na hada kai da gwamnatoci

Sanarwar da shugaban sashen hulda da jama’a na KEDCO, Sani Bala ya kara da cewa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na tattaunawa da gwamnatocin jihohi guda 3 domin magance matsalar wuta a yankunansu.

Ya kara da cewa kamfanin ya samar da sabon tsarin tattara kudin wuta domin dakile karkatar da kudin da wasu jami’anta ke yi, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

Sanarwar ta ce Manajan Daraktan hukumar, Alhaji Abubakar Yusuf ne ya bayyana hakan inda ya kira sabon tsarin da IRecharge product.

Ya ce sabon tsarin zai ba masu hulda da KEDCO damar biyan kudin wuta ta hanyoyi daban-daban har da WhatsApp, USSD da banki.

Gwamnati za ta dawo da wuta Sokoto

A baya mun kawo cewa gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta ce za ta dawo da lantarki ga kananan hukumomin da suka shafe shekaru ba wuta a jihar Sokoto.

Ministan makamashi Adelabu Adebayo ne ya lokacin da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ziyarce shi a ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.