Hukuncin Kisa: AbdulJabbar Kabara da Lauyansa sun ki Bayyana gaban Kotu

Hukuncin Kisa: AbdulJabbar Kabara da Lauyansa sun ki Bayyana gaban Kotu

  • Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da lauyansa, Barista Sadiq Yusuf sun gaza bayyana a zaman kotun ci gaba da sauraron daukaka karar da ya shigar gabanta
  • Tun da fari Sheikh AbdulJabbar ya daukaka kara yana kubalantar hukuncin kisan da babbar kotun shari’ar musulunci ta yanke masa bayan tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi
  • Kotun ta ce ta tabbatar da zargin da ake yiwa malamin na batanci ga janibin Ma’aiki (SAW), lamarin da AbdulJabbar ya ce ba gaskiya ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da lauyansa sun ki bayyana a zaman kotun da ya shigar yana kalubalantar hukuncin kisan da wata kotu ta yanke masa a Kano.

Kara karanta wannan

Kin bayyanar Yahaya Bello a kotu ya fusata alkali, an sake ba EFCC damar kama shi

Bayan kotu ta hallara ne a jiya Alhamis, kuma an kira shari'ar, sai aka ga lauyan malamin, Sadiq Yusuf, da Sheikh Abdul-Jabbar Nasiru Kabara ba su shiga kotun ba.

Shiekh AbdulJabbar Nasiru Kabara
AbdulJabbar Kabara da Lauyansa ba su halarci zaman kotu ba Hoto: Politics Digest
Asali: UGC

Ina Sheikh Abduljabbar Kabara ya shiga?

Tuni lauyan gwamnati, Barista Bashir Saleh, ya yi amfani da damar wajen mika rokonsu na neman kotun ta kara musu lokaci don yin suka ga rokon da masu kara suka yi, Kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abduljabbar Kabara ya tunkari kotun ne yana kalubalantar hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotun shari’ar musulunci ta yi masa.

AbdulJabbar Kabara ya zargi kotu da kwange

Tun da fari dai malamin ya daukaka kara kotun ne yana kalubalantar sashi na 275 da na 375 na kundin shar'iar da ake yanke masa hukunci da su.

Ya yi zargin cewa an yi kwange a wasu daga sadarar da aka yi amfani da su wajen yanke masa hukuncin kisa, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba da belin tsohon minista Hadi Sirika da ɗiyarsa, an kafa sharuda

A zaman kotun na ranar Alhamis karkashin jagorancin Masu Shari’a Nasiru Saminu da Aisha Mahmood, an amince da rokon lauyoyin gwamnati na kara musu lokaci.

Daga bisani kotu ta dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Mayu, 2024.

Ranar shari’ar AbdulJabbar Kabara a Kano

Mun ruwaito muku cewa kotun musulunci ta sanya ranar ci gaba da sauraron daukaka karar da Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar gabanta.

Malamin na neman kotu ta janye hukuncin kisa da wata kotun addinin musulunci ta yanke masa bayan ta ce an same shi da laifin batanci ga ma’aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.