Bankin CBN Ya Bayyana Abin da Ke Kawo Masa Ciwon Kai da Manoman Jihar Kano

Bankin CBN Ya Bayyana Abin da Ke Kawo Masa Ciwon Kai da Manoman Jihar Kano

  • Shugaban bankin CBN reshen Kano Alhaji Umar Ibrahim Biu ya roki bankuna a jihar su shiga tsarin bayar da rance ga manoma
  • Shugaban ya ce rokon ya zama wajibi duba da cewa kananan bankunan masana’antu ne kadai ke taka rawa a cikin tsarin
  • Bankin na CBN na ganin cewa shigar da bankunan cikin wannan tsari zai kara bunkasa sha’anin noma a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Babban bankin kasa CBN ya bukaci bankunan kasuwanci a jihar Kano da su shiga cikin tsarin nan na bada bashin noma domin bunkasa fannin noma a kasar nan.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

Shugaban bankin reshen Kano Alhaji Umar Ibrahim Biu ne yayi wannan roko a wajen liyafar cin abincin dare tare da bada kyaututtuka da bankuna suka shirya a jihar.

Shugaban CBN
CBN ya shawarci bankuna a Kano shiga tsarin bayar da bashi ga manoma Hoto: CBN
Asali: Facebook

Bankin CBN ya koka da manoman Kano

Biu yace rokon ya zama wajibi duba da cewa kananan bankunan masana’antu ne kadai ke taka rawa a cikin tsarin, kamar yadda Punch News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya kara da cewa shigar bankunan cikin wannan tsari zai kara bunkasa sha’anin noma a jihar Kano

Takardar neman aron kudin noma

Bayanai na nuna cewar a shekarar 2023, mutane 575 ne kacal suka samu rabauta da bashin noman a Kano da kudin da aka bayar a matsayin bashin ya kai N94, 289, 000.

Tsarin dai an kirkireshi ne domin saukakawa manoma samun bashi, amma karancin shigar bankunan kasuwanci cikinsa na zama wani babban tarnaki, tare da takaita yawan manoman da zasu amfana karkashin tsarin.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba yayin da 'yan banga suka bindige babban jami'in ɗan sanda a Taraba

Manoman Kano sun barar da dama

A shekarar 2021 ma, sai da bankin na CBN ya bayyana rashin jin dadin yadda manoma a yankin kudu maso gabas ke kin shiga tsarin karbar rancen noma, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Saboda haka Alhaji Ibrahim Biu shugaban babban bankin kasa CBN reshen Kano ya shawarci masu sha’awar karbar bashin noman da su tuntubi cibiyoyyin kudi dake kusa dasu domin karbar takardar neman bashin kyauta.

Majalisa na binciken Buhari

Mun kawo muku a baya cewa majalisar dattawa za ta fara binciken bashin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ciwo a babban bankin kasa CBN.

Sanata Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta Arewa ya gabatar da rahoton da ya tabo bashin da CBN ya ba gwamnatin Najeriya har Naira Miliyan 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.