Tsohon Minista Hadi Sirika Ya Kafa Misali da Annabawa Yayin da Ya Gurfana a Gaban Kotu

Tsohon Minista Hadi Sirika Ya Kafa Misali da Annabawa Yayin da Ya Gurfana a Gaban Kotu

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya yi magana kan yiwuwar ya tsinci kansa a gidan gyaran hali yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotu
  • A wani bidiyo da aka sanya a manhajar X an nuna tsohon ministan yana kwantar da hankalin ɗiyarsa yayin da suke cikin kotu
  • Hadi Sirika dai yana fuskantar shari'a kan badaƙalar N2.8bn tare da ɗiyarsa Fatima da wasu mutum uku a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika wanda ke fuskantar shari'a kan zargin badaƙalar N2.8bn, ya nuna cewa a shirye yake yaje gidan kurkuku.

Hadi Sirika, ɗiyarsa Fatima da wasu mutum uku an gurfanar da su a ranar Alhamis a gaban mai shari'a Sylvanus Orji na babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

An gurfanar da Hadi Sirika a kotu
EFCC na zargin Hadi Sirika da karkatar da makudan kudi Hoto: @TosinOlugbenga
Asali: Twitter

Wani bidiyo na tsohon ministan yana magana da lauyoyinsa a cikin kotu ya bayyana a ranar Alhamis a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadi Sirika ya yi magana a kotu

A cikin bidiyon an nuna tsohon ministan yana kwantar da hankalin ɗiyarsa yayin da ta shiga cikin damuwa.

"Ya isa Fatima, ya isa haka. Ya isa haka mana. Annabawa ba sun je kurkuku ba."
"...Kuma sun gama na su. Su tsaya su ga abin da Allah zai yi."

- Hadi Sirika

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) na zargin tsohon ministan, ɗiyarsa, sirikinsa da kamfanin Al-Duraq Investment Limited, bisa badaƙalar N2.8bn.

An ba da belin tsohon ministan jirage

A halin da ake ciki, kotu ta ba da belin kowannensu kan kuɗi N100m tare da kawo mutum biyu da za su tsaya musu.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba da belin tsohon minista Hadi Sirika da ɗiyarsa, an kafa sharuda

Haka kuma, a sharuɗan belin, kotun ta haramta wa waɗanda ake tuhuma fita ƙasashen waje ba tare da izininta ba.

Kotun ta kuma ja kunnen waɗanda ake tuhumar da cewa za a tsare su a gidan gyaran hali da zarar sun saɓa ɗaya daga cikin sharuɗan belin da ta sanya.

EFCC ta tsare Hadi Sirika

A wani labarin kuma, kun ji cewa cewa hukumar EFCC ta tsare tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan zargin badaƙalar N2.8bn.

EFCC ta gudanar da bincike kan zargin rashawa da bayar da haramtattun kwangiloli ga diyarsa, 'yan uwansa da abokan hulɗarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng