'Yan Majalisa Sun Nemi a Komawa Sojojin Haya a Kasashen Waje Saboda Rashin Tsaro
- Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauko hayar sojoji daga kasashen ketare duba da halin tsaro da kasar nan ke ciki
- Dan majalisa mai wakiltar Chibok, Domboa da Gwoza a majalisar Ahmed Jaha ne ya mika bukatar domin su taimaka wajen magance rashin tsaro
- Ahmed Jaha ya zargi Jami’an tsaron Najeriya da gaza yin katabus wajen kawo karshen matsalar tsaro duk da makudan kudin da ake zubawa a fannin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauko sojojin haya daga kasashen waje domin su taimaka wajen kawo karshen rashin tsaron da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar nan.
'Dan majalisa mai wakiltar Chibok, Domboa da Gwoza a majalisar wakilai, Hon. Ahmed Jaha ne ya mika bukatar nan.
Hon. Jaha ya kawo shawara a majalisa
Hon. Ahmed Jaha ya tunatar da majalisa cewa ko a lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, gwamnati ta dauko hayar sojojin, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan Majalisar ya kara da cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kore sojojin hayar da aka dauko a wancan lokaci.
“Sojojin Najeriya sun gaza,” Majalisa
'Dan majalisar wakilai mai wakiltar Chibok, Domboa da Gwoza a jihar Borno, Ahmed Jaha ya zargi jami’an tsaron Najeriya da gaza magance rashin tsaro.
A zaman majalisa da aka yi a Talatar nan, ya bayyana rashin jin dadi kan yadda rashin tsaro ke ci gaba da addabar ‘yan Najeriya duk da makudan kudin da ake warewa bangaren.
A rahoton da Punch News ta wallafa, Ahmed Jaha ya bayyana cewa daga shekarar 2015 zuwa 2023, an sanya zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan 19 a bangaren tsaron Najeriya.
'Dan siyasar ya shawarci gwamnati ta dauko sojojin haya domin magance matsalar cikin gaggawa.
Majalisa ta magantu kan satar dalibai
Mun ruwaito muku cewa majalisar wakilan Najeriya ta bayyana takaicin kan yawaitar hare-haren da yan bindiga ke kaiwa makarantu.
Ta kuma wajabtawa kwamitocinta na rundunar sojin ƙasa, sojin ruwa, sojin sama, ƴan sanda da kwamitin tsaro su zauna da hafsoshin tsaro domin a lalubo bakin zaren.
Asali: Legit.ng