Rashawa: Tsofaffin Gwamnoni 6 da EFCC Ta Taba Kamawa da Laifin Sata a Najeriya
A tsawon shekaru da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta yi na yaki da cin hanci da rashawa, ta zargi tsofaffin gwamnoni sama da 30
- A cikin zarge-zargen da ta yi na tsawon shekaru, ta yi nasarar gurfanarwa tare da daure shida bisa kamasu da laifin sama da fadi da dukiyar gwamnati
- Sai dai a cikin tsofafaffin gwamnonin da aka kama da laifin, an kyale sama da rabinsu sanadiyyar afuwa da wasu shugabbannin kasa suka musu da kotuna
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tun kafa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFFC) a shekarar 2003 take kokarin kamawa da hukunta tsofaffin gwamnoni kan badakala da dukiyar al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin shekaru 21 da kafa hukumar, ta zargi tsofaffin gwamnoni guda 39 da zagon kasa kuma ta yi nasarar kama guda 6 da laifi dumi-dumu.
Sauran 33 kuma ana ta kai komo wurin kokarin kama su da gurfanar da su a gaban kotuna, cewar jaridar the Cable.
Tsofaffin gwamnoni 6 da EFCC ta kama
1. Tsohon gwamnan jihar Plateau, Joshuwa Dariye
A shekarar 2007 aka gurfanar da Joshua Dariye a gaban kotu bisa zarge-zarge guda 23 ciki harda almundanar Naira biliyan 1.62.
Shari'a tsakanin EFCC da Joshua Dariye ta dauki tsawon shekaru takwas, sai daga bisani aka yanke masa hukunci a shekarar 2018.
Kotu ta yanke masa hukuncin zama gidan kaso na shekaru 14 bisa laifin cin amana da kuma shekaru biyu bisa badakala da dukiyar al'umma.
Amma daga baya aka rage hukuncin shekaru 14 ya dawo 10, shekaru biyun kuma ya dawo shekara daya, cewar.
Sai dai a ranar 8 ga watan Ogusta na shekarar 2022, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa afuwa aka sake shi tare da Jolly Nyame daga gidan gyaran hali.
2. Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame
Hukumar EFCC ta zargi Jolly Nyame da karkatar da Naira biliyan 1.64 a lokacin da yake gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007.
Bayan shafe shekaru 11 ana shari'a, daga karshe kotu ta kama shi da laifi tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2018.
Bayan ya ɗaukaka kara sai kotu ta rage masa daurin zuwa shekaru 12 daga nan kuma ya kara daukaka kara a shekarar 2020 amma bai samu nasara ba.
Bayan ya yi shekaru biyu a gidan gyaran hali, a shekarar 2022 tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafe masa aka sake shi..
3. Tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion
Bayan ya kammala gwamma a jihar Edo daga 1999 zuwa 2007, EFCC ta zargi Lucky Igbinedion da karakatar da kudi naira biliyan 2.9.
A shekarar 2008 wata kotu ta kama shi da laifi tare da yanke masa zaman gidan kaso na watanni shida ko biyan tarar Naira miliyan 3.5.
Har ila yau, kotun ta kwace kudi naira miliyan 500 da manyan kadarori guda uku ciki harda gida guda daya a Abuja daga wajensa.
A shekarar 2021, hukumar EFCC ta kara kama shi bisa zargin karakatar da kudi naira biliyan 1.6.
4. Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori
Bayan kammala gwamnatinsa daga 1999 zuwa 2007, a shekarar 2012, aka kama James Ibori da zargin karkatar da kudi Euro miliyan 50.
Wata kotu a Birtaniya ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 amma a shekarar 2016 bayan shafe rabin shekarun aka masa afuwa.
Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya zargi tsohon gwamnan da neman ba shi cin hancin dala miliyan 15 domin yafe masa.
5. Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha
Bayan hawa mulki a shekarar 1999, an tsige gwamna Diepreye Alamieyeseigha a shekarar 2005 kuma a shekarar ne EFCC ta kama shi bisa badakalar kudi.
Duk da cewa a karon farko jami'an tsaron kasar Birtaniya sun kama shi da laifuffukan da ke da alaka da badakalar kudi guda uku wanda kudin ya kai Euro miliyan 1.8 a cewar jaridar the Guardian.
A shekarar 2007, ya amsa laifinsa kuma an yake masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kaso.
Bayan samun mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, a shekarar 2013 aka masa afuwa kuma hakan yasa aka sake shi.
A watan Fabrairun 2023 ne jaridar Premium Times ta ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta dawo da dala miliyan 1 ga gwamnatin Najeriya da tsohon gwamnan ya sace.
6. Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu
Bayan kammala mulki a jihar Abia, an zargi Orji Kalu da karkatar da kudi naira biliyan 7.1 daga asusun jihar.
A shekarar 2019, kotu ta kama shi da laifi inda kuma ta yanke masa daurin shekaru 12 a gidan gyaran hali.
Biyo bayan shari'ar, a ranar 8 ga watan Mayun shekarar 2020 kotun Allah ya isa dake Abuja ta rusa hukuncin kuma daga nan aka sake shi.
Duk da cewa EFCC ta magantu kan sake bincikensa saboda badakalar Naira biliyan 6.7 amma a watan Maris din wannar shekarar kotu ta dakatar da EFCC daga hakan.
An amice EFCC ta kama Yahaya Bello
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta samu izinin kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Mai shari’a Emeka Nwite na babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ya ba EFCC takardar izinin kamun a yammacin ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu.
Asali: Legit.ng