Kotun koli ta tabbatar da hukuncin zaman kurkukun shekara 12 kan Jolly Nyame

Kotun koli ta tabbatar da hukuncin zaman kurkukun shekara 12 kan Jolly Nyame

Kotun kolin Najeriya a ranar Juma'a, ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 12 kan tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, kan laifin badakala da babakere.

Alkalan kotun kolin biyar da suka zauna kan lamarin karkashin jagoranin Jastis Mary Odili, sun yi ittifakin cewa babu wani hujja kwakkwara na soke shari'ar kotun daukaka kara da ta kama Jolly Nyame da laifin.

Alkali Amina Augie da ta karanto shari'ar ta ce babu kamshin gaskiya cikin kalaman Jolly Nyame na kokarin wanke kansa daga laifin da aka kamashi da shi.

Amma kotun kolin ta ce kotun daukaka kara ta yi kuskure wajen cin tsohon gwamnan tarar kudi. Saboda haka, kotun ta soke shari'ar tara da aka bukaceshi ya biya kan babakeren da ya yiwa baitul malin jihar Taraba lokacin mulkinsa.

Kotun koli ta tabbatar da hukuncin zaman kurkukun shekara 12 kan Jolly Nyame
Kotun koli ta tabbatar da hukuncin zaman kurkukun shekara 12 kan Jolly Nyame
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Maina zai cigaba da zama a Kurkuku, ya gaza cika sharrudan beli

A ranar 3 ga watan Maris 2018, kotu ta yanke hukuncin daurin gidan yari na tsawon shekaru 12.

Hukumar EFCC tayi karar Jolly Nyame bisa zargin cin amana da karkatar da kudin Gwamnati tun 2010. Lauyan da ya shigar da karar Rotimi Jacobs ya kawowa Kotu shaidu akalla 14 da su ka tabbatar da zargin da ke kan wuyan tsohon Gwamnan.

Lauyan da ke kare tsohon Gwamnan watau Olalekan Ojo ya bayyanawa Kotu cewa ayi watsi da shaidar da EFCC ta kawo domin akwai tafka-da-warwara a bayanan. Lauyan yace babu wata hujjar gaske da ke nuna cewa Nyame ya saci kudin Jihar Taraba.

EFCC na zargin Nyame da sace Naira Biliyan 1.641 a lokacin yana Gwamna don haka aka nemi Alkali mai shari’a ya garkame shi cikin gidan yari ba tare da bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel