Bayan fitowa daga gidan yari, an sake gurfanar da Orji Kalu a kotu

Bayan fitowa daga gidan yari, an sake gurfanar da Orji Kalu a kotu

Mai tsawatarwa a Majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya dira babban kotun tarayya dake Abuja don gurfanar da shi kan zargin almundahanar biliyan 7 kudin jihar Abia da yayi yana gwamna.

Tsohon gwamnan na gurfana gaban, Alkali Inyang Ekwo, ranar Talata, 2 ga Febrairu, 2021.

Za ku tuna cewa an kama Orji Uzor Kalu, wanda yayi gwamnan jihar Abia daga 1999 zuwa 2007, da laifin almundahana kuma aka jefa shi kurkukun shekara 12.

Amma bayana watanni shida a Kurkuku, kotun koli ta bada umurnin sakinsa bisa wani kuskure da akayi a kotun daukaka kara.

Tun lokacin hukumar EFCC tayi alkawarin sake gurfanar da shi.

Kalli bidiyonsa a kotu:

Source: Legit.ng

Online view pixel