Jerin Kudin Haraji 5 da CBN Ya Amince Bankuna Su Cire Daga Asusun ’Yan Najeriya
- Akalla kudaden haraji 5 ne bankuna ke cire daga asusun abokan huldarsu idan sun yi hada-hadar kudade ta intanet, musamman tura kudi
- Idan ba a manta ba, a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, babban bankin Najeriya ya ba bankuna umarnin fara cire harajin tsaron yanar gizo
- Legit Hausa ta tattaro jerin harajin da bankuna ke cajar 'yan Najeriya da kuma adadin kudin da ake caja kan kowanne haraji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayar da umarni ga dukkan bankunan da ke aiki a cikin kasar da su sanya harajin 'kudin tsaron yanar gizo' kan abokan huldarsu.
Harajin tsaron yanar gizo a bankuna
Legit Hausa ta ruwaito babban bankin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, ya ce za a fara cire kudin harajin ne nan da makonni biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ba da umarnin daftarin zuwa ga dukkan bankunan kasuwanci, ƴan kasuwa, bankuna marasa karbar kudin ruwa, da bankunan biyan kuɗi na intanet.
Akwai kudaden haraji biyar da babban bankin ya amince bankuna su cire daga asusun ‘yan Najeriya yayin hada-hadar kudi kamar yadda jaridar The Nation ta tattara.
1. Harajin kudin tsaron yanar gizo (0.5%)
A jiya Litinin CBN ya saka wannan harajin kan dukkanin hada-hadar kudaden intanet, inda za a rika cire 0.5% na kudaden da aka yi hada-hadarsu.
Misali:
- Ana cire harajin N5 a kan hada-hadar N1,000
- Ana cire harajin N50 a kan hada-hadar N10,000
- Ana cire harajin N500 a kan hada-hadar N100,000
Har zuwa abin da ya fi hakan.
2. Harajin tura kudi
Jaridar The Punch ta ruwaito a duk lokacin da abokin hulda ya tura kudi daga bankinsa zuwa wani bankin, ana cire wasu 'yan kudade a matsayin harajin tura kudi.
Misali:
- Ana cire harajin N10 a kan N1 zuwa N5,000 aka tura.
- Ana cire harajin N25 a kan kudin da aka tura daga N5,001 zuwa N50,000
- Ana cire harajin N50 a kan kudin da aka tura da suka haura N50,000
3. Harajin buga hatimi
Harajin buga hatimi wai nau'in haraji ne da ake biya a kan hatimin da bankuna ke bugawa kan takaddun hada-hadar da abokan hulda suka gudanar a intanet.
Ana cire harajin N50 na buga hatimi a kan hada-hadar kudi daga N10,000 zuwa N10,000,000.
4. Harajin tura saƙon kar-ta -kwana (SMS)
A duk lokacin da abokin hulda ya yi hada-hadar kudi, banki na tura masa sakon kar ta kwana na bayanin wannan hada-hadar, ana cire wasu 'yan kudade a matsayin haraji.
Ana cire harajin N4 a kan kowane sanarwar kammala hada-hadar kudi da banki ya yi.
5. Harajin kimar hada-hada (VAT)
Ana cire harajin VAT a kan dukkanin kudaden da aka caji abokin hulda yayin hada-hadar kudi a intanet.
Misali:
- Ana cire harajin N0.75 a kan N10 da aka caja na tura kudi.
- Ana cire harajin N1.875 a kan N25 da aka caja na tura kudi.
- Ana cire harajin N3.75 a kan N50 da aka caja na tura kudi.
Bankuna za su fara cajar kudin ajiya
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito bankunan Najeriya za su cajar kudaden da abokan hulda suka je ajiye wa a bankunan da suka haura N500,000.
A yayin da za a caji 2% na adadin kudaden da suka haura N500,000 ga daidaikun mutane, bankuna za su caji 3% na adadin da ya haura N3,000,000 ga kamfanoni.
Asali: Legit.ng