Gwamnatin Kano ta Fadi Dalilin Fara Rajistar Gawan da Ake Binnewa a Makabartu
- Gwamnatin Kano za ta bude rajista a makabartu domin daukar alkaluman mamatan da ake binnewa da zimmar samun sahihan bayanai kan yawan mutuwa a jihar
- Kwamishinan lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a garin Kura inda ake zaton wasu mutum 40 sun rasu kwanakin baya saboda bullar wata cuta
- Labaran ya ce an dauki matakin ne domin samun tabbacin yawan wadanda ake binnewa, da kuma gujewa labaran karya kan yawan mamatan da ake samu a jihar Kano
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano- Gwamnatin Kano ta samar da littafin yin rajistar adadin mamatan da ake binnewa a makabartun dake fadin jihar.
Kwamishinan lafiya a Kano, Dr. Labaran Abubakar Yusuf ne ya tabbatar da daukar matakin yayin taron makon allurar riga-kafi a Afrika a karamar hukumar Kura.
Tribune Nigeria ta wallafa cewa kwamishinan ya ce daukar matakin zai taimaka kwarai wajen tantance ainihin adadin wadanda ake binnewa a makabartun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan daya daga hanyoyin da gwamnati ta bullo da shi ne wajen magance labaran karya kan yawaitar mutuwa a jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta magantu kan yawan mutuwa
Kwamishinan lafiya na Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa sun samu labarin yawan mace-mace a fadin jihar.
Ya ce wasu daga labaran ba gaskiya ba ne, inda ya yi misali da kauyen Gun-dutse da ke kura da aka ruwaito cewa an samu labarin akalla mutane 40 sun rasa rayukansu saboda bullar bakuwar cuta.
Ana yada labaran mace-macen karya a Kano
Leadership News ta tattaro cewa kwamishinan ya musanta hakan, inda ya ce mutum shida ne suka rasu.
Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya kuma koka kan yadda labaran karya ke kawo cikas wajen gudanar da ayyukan ma'aikatarsa.
A jawabin da ya yi, kwamishinan ya yi kira na musamman ga al'umma su guji yada labaran da ba su da tabbacinsa.
An bayyana dalilin rashe-rashe a Kano
A baya kun ji gwamnatin jihar Kano ta dora alhakin yawaitar rashe-rashe da ake yi a jihar kan tsananin zafin da ake fama da shi.
Kwamishinan lafiya a jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya ce duk da cewa ana tsananta bincike kan musabbabin rasuwar, ba zai rasa nasaba da tsananin zafin da ke tsose ruwan jikin mutane ba.
Asali: Legit.ng